Gina Rugan Makiyaya: Yunkuri Ne Mai Kyau, Amma An Yi Hanzari – Abdul’aziz Mai Maggi

Alhaji Abdul’aziz Salisu Mai Maggi, Sarkin Arewan Anguwar Mu’azu, Shahararren Manomi ne, kuma dan kasuwa, har ila yau ga shi daya daga cikin iyayen al’umma. Ya fadi albarkacin bakin sa ne a kan wannan batu da ake ta kai komo a kansa, watau batun kafa RUGA, ko mu ce Rugagen Makiyaya. Ga yanda ya bayyana na shi fahimtar a kan wannan batu ga, LEADERSHIP AYAU JUMA’A, lokacin da ya zanta da wakilinmu Umar A Hunkuyi, a fadarsa.

A sha karatu lafiya:

An jima ana samun takun saka da rigingimu a tsakanin Manoma da Makiyaya a wasu sassan kasar nan, inda har abin ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a wurare da yawa. Daga bisani gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti wanda ya yi bincike da nazarin nemo hanyar warware abin da kan janyo ire-iren wannnan rikicin. Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar akwai batun kafa Rugage, watau inda Makiyayan za su zauna da dabbobin su suna kiwo. Gwamnatin tarayya tana kan fara aiwatar da shirin ne sai wasu gwamnatocin Jihohi, kungiyoyi da wasu al’ummun musamman a kudanci da tsakiyar arewacin kasar nan suka nuna su ba su amince da a kafa masu wadannan rugagen ba. Hakan ya kai ga gwamnatin tarayya har ta dakatar da aiwatar da shirin, a matsayinku na Shugabannin al’umma, Manomi, Dan kasuwa, ya ka fahimci wannan lamarin ne?

Da farko in muka lura da wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na samar da matsuguni ga Makiyaya, tabbas wannan yunkuri ne mai kyau na ganin an dakile rigingimun da suka yi ta aukuwa da ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. Amma daya daga cikin hanzarin da aka yi na gabatar da wannan shirin shi ne, kamata ya yi a dauki matakin wayar da kai tukunna, sannan a fara shirin ta inda suka san mahimmancin abin, domin wanda ya san mahimmancin abu shi ne kake ba shi, amma mutumin da shi bai fahimce ka ba, bai kuma shirya ya ma fahimce kan ba, to ba yanda za ka yi ka nuna ma shi mahimmancin abin nan.

Akalla wannan abin da aka so a yi kamata ya yi a fara gabatar da shi a arewacin Nijeriya, inda suka san darajan kiwon da inda suke kiwon, in aka yi daga nan din ana iya kai shi ko’ina, watakila ma su za su nema da lallai a kai masu can din. Amma tashin farko da ake son ayi abin da yawa, sai suka yi wa abin gurguwar fahimta, saboda da yawa wasunsu gani ma suke yi kamar ana son a raba su da filayen su ne ko kuma ana son a shigo masu da wani abu wanda su ba su aminta da shi ba. Wannan abu ne mai kyau, amma yanda aka shigo da shi ne tun farko, ko kuma sigar da ita gwamnati ta yi amfani da ita ne ta haifar da rashin fahimta a cikin al’amarin.

…A nan, kamar cewa kake yi a dawo da shirin nan arewacin arewa inda aka san kimar kiwo can kuma a rabu da su tun da ba sa so?

Haka ne, tabbas tun da in mun lura da rigingimun duk da ake samu a tsakanin Manoma da Makiyaya, duk kan wuraren kiwo ne da kuma filayen noma, a baya akwai labi-labi da aka samar wanda ke baiwa masu kiwon daman yin kiwon su ba tare da wata matsala ba, amma sai daga baya duk aka yi watsi da su, al’umma suna yin noma duk inda suka ga dama, ita kuma hukuma ta kyale. Shi mai kiwo a kowane lokaci yana son inda zai ratsa ya wuce da dabbobinsa, kuma babu, don haka sai wannan abin ya haifar da babban rigima a tsakani.

Yawanci Makiyayan nan suna tafiya kudancin kasar nan ne domin neman ciyawa kasantuwan wajajen kurmi ne wanda kusan a kowane lokaci akwai ciyawar a cikin sa, to in an ce duk su dawo nan arewacin arewa, ba ka ganin ana iya samun matsala?

Ai yanzun an ci gaba sosai, domin in mun dubi yanda wasu kasashen suke yin noma, ana yin noma ne na zamani, a kan yi noman ciyawa domin kadai a baiwa dabbobi su ci. Nan in ka tsallaka su Jamhuriyar Benin ko Ghana za ka taras suna yin noma ne na zamani, akwai ma kasar da na sami labarin su neman ma makiyayan suke yi da su je can su zauna da dabbobin su su yi kiwo, sun tsara masu komai za su rika biyan haraji, sun samar masu da ruwa da wuraren kiwo na zamani har ma da wuraren da za su yi noma in suna bukata. Kuma dan abin da za su rika badawa din nan bai kai ya komo ba, a karshe dai mutanan kasan ne za su rika amfana da su.

A nan arewacin Nijeriya din akwai wajen da in har za a inganta shi ya isa baki-dayan wannan shirin, ba ma sai an je wani nesa ba. Amma dai babban abin shi ne, wannan shiri na Ruga da ake son a bullo da shi, ana son yinsa ne domin a kaucewa fadace-fadacen da ke aukuwa a tsakanin Manoma da Makiyaya. To kuma tun da haka ne, abin yana kawo matsala a wasu wuraren, ko kuma ba su fahimci shirin ba. To ni a nawa fahimtar, in aka fara aiwatar da shi a nan, mutane suka saba aka ga amfanin abin, ina da tabbacin zuwa gaba wasu da suka yi wa abin gurguwar fahimta su za su rika ruguguwar a zo a yi masu.  Amma a halin yanzun yanda abin ya zama, nan din dai da muka san darajan abin, nan ne muka fi da bukatan a yi shi, sabanin yanda a halin yanzun gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar cewa ta dakatar da shirin, akwai bukatar a kawo abu ne inda aka san mahimmancin shi, wannan shi ne zai taimaka da gasken gaske wajen cin gajiyar shi wannan shirin.

Exit mobile version