Muhammad Sani Chinade" />

Ginin Kasuwar Damaturu Ya Kankama

A halin da ake ciki tunin aiki gina sabuwar kasuwar garin Damaturu Shalkwatar Jihar Yobe ya yi nisa amma har ya zuwa yanzu nafi yawa daga cikin masu shagunan da aka rushe don gina sabuwar kasuwar na kokawa bisa ga rashin biyansu kudadensu na shagunan su da aka rushe tare da zargin cewar gwamnatin Jihar ta yi ko oho bisa biyansu hakkokinsu duk cewar a cikin bayaninsa ga ‘yan kasuwar a cikin wani shiri Na tambaya da amsa da gidan Rediyo mallakar Jihar (YBC ) ya shirya yadda mai girma gwamna. Jihar Mai Mala Buni ya halatta, ya ambata cewar a sanin sa tuning an cire kudaden ma’aikatan don biyansa hakkokinsu.

Kan haka ne wakilinmu ya samu tattaunawa da shugaban kungiyar  ‘yan Kasuwar Damaturu Alhaji Kale Alhaji Bukar dangane da wannan lamari a matsayinsa na Wanda ke cikin mambobin kwamitin biyan ‘yan kasuwar hakkokinsu, yadda shugaban ya yi Karin haske kan wannan batu da cewar, a saninsa an gwamnatin Jihar Yobe lokacin tsohon gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ta ce ta ware kimanun Naira Miliyan 180 ne don biyan ‘yan kasuwar hakkokinsu.

Shugaban ya kara da cewar, cikin shaguna 658 da aka da su a kasuwar an biya ma su shaguna 248 zunzurutun kudi har Naira Miliyan 120 saura shaguna 409 da masu shi ba a biya su ba wadda kudin da ya rage a cewar kwamitin saura Naira Miliyan 66 wadda su din ma har ya zuwa yau din.

Alhaji Kale ya kara da cewar, kan wannan lamari shi da kansa ya jagoranci tawagar wasu ‘yan kasuwar ya zuwa zauren majalisar dokokin Jihar don mika kokensu ka kakakin majalisar yadda kakaki. Majalisar ya basu tabbacin yin wani abu akai, hakan kuwa aka yi domin kuwa majalisar ta kai ga saduwa ga gwamna Buni, ya kuma tabbatar da yin wani Abu akai.

Ya kara da cewar,  gwamna Mai Mala a hirarsa a cikin gidan Rediyon Jihar ya bayyana cewar,  a saninsa sun kammala biyan dukkannin hakkokinsu ‘yan kasuwar to amma kuma zai sake duba lamarin don yin wani abu a kai.

Don haka ne a cewarsa shi kansa ba a kai ga biyan sa  kudin shagonsa ba har ya zuwa yanzu ballantana ma a hada baki da shi don danne hakkokin ‘yàn uwansa ‘yan kasuwar kamar yadda wasu ke zargin sa a kai saboda rashin sani.

Shugaban ya yi da babbar muryaa gs gwamnan Jihar Alhaji Mai Mala Buni kan ya kawo musu dauki ta wajen gano su waye hakkokin ’yan kasuwar kW hannunsu domin a cewaraa da yawa cikin ‘yan kasuwar sanadiyyar hakan sun rasa rayukansu yayin da wassu kuma suka rasa lafiyarsu.

Kale ya kara da cewar, duba da yadda lamurra suka tabarbare kan hakan da yawan ‘yan kasuwar sun karye wato jarukansu sun Kate ta yadda babu a kanti babu a kanta.

Exit mobile version