Khalid Idris Doya" />

Girgizan Kasa Ya Kashe Mutane 380 A Kasar Indonesia

An tabbatar da mutuwar, mutune dari uku da tamanin (380) bayan da bala’in tsunami tare da girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta afka wa wani babban birnin a kasar Indonesia a ranar Jumma’ar da ta wuce.

Igiyoyin ruwa sun yi tunkoro har zuwa tsayin-tsayin mita uku hakan ya sa ruwa ya shafe tsibirin Sulawesi.

Hotunan bidiyon da aka sanya a kafafan sada zumunta sun nuna yadda mutane ke ta kururuwa tare da tserewa a cikin dimuwar neman ceto.

Dubban gidaje da asibitoci da ote-otel da kuma shaguna ne suka rushe sakamakon girgizar kasar.

Masu aiki ceto na ta kokari wajen ceto mutane da lamarin ya rutsa da su, kodayake suna fuskantar ‘yan wasu matsaloli a aikin ceton na su.

An rufe babbar hanyar da ta bulla zuwa birnin Palu saboda zaftarewar kasa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa ransu sakamakon girgizar kasar zai iya karuwa, kuma akwai mutum akalla 540 da suka samu raunuka, yayin da kuma ba a gano wasu mutum 29 ba.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawan, Sutopo Purwo Nugroho ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, an gano wasu gawawwakin a gefen gabar teku.

Ya kuma ce koda al’amarin ya fara faruwa sama-sama a ranar Jumma’ar, mutane sun ci gaba da harkokinsu a bakin ruwa, amma kuma da lamarin ya munana sai suka fara tserewa.

Wasu mutane dai sun tsira da ransu ne bayan da suka dirgo daga wani gini mai nisan mita shida.

Babban asibitin birnin ya lalace sakamakon girgizar kasar, inda wasu hotuna da aka nuna a kafar talabijin din kasar suka nuna yadda ake kula da marassa lafiya a wajen asibitin.

Biranen Palu da Donggala na dauke da mutane fiye da dubu 600.

Shugaba Joko Widodo, ya ce an tura sojoji wuraren da lamarin ya faru domin taimaka wa jami’an agaji a aikin ceton da suke.

Tuni dai aka rufe babban filin jirgin saman Palu tun bayan afkuwar girgizar kasar. Kazalika an tura wasu jirage soji domin kai kayan agaji ga wuraren da alamarin ya afku daga Jakarta.

 

 

 

Exit mobile version