Girki Adon Mace

Wainar Dankali

Daga Bilkisu Tijjani Kassim

Wainar Dankali

Abubuwa da Uwargida za ta tanada

Dankalin turawa, Attarugu, Albasa, Maggi, Mai, Kwai

Yadda uwargida za ta hada Wainar Dankali:

Za ki samu dankalinki mai kyau ki feraye shi ki wanke sai ki nika shi ya yi laushi da kauri kada ki saki ruwa wurin nikan, sai in injin nikan ya cije, daga nan sai ki sa kadan, bayan nan sai ki zuba a roba ki yanka albasa ki saka magi da gishiri da kuri in kina da dan wani kayan kamshi shi ma sai ki sa ki fasa kwanki kamar biyu haka sai ki dauko attarugunki ki wanke shi, ki daka shi ki zuba daidai yadda kike so. Sannan ki dora Tandar wato abin suyar masarki a wuta ki zuba Mai kamar cokali biyu, idan ya yi zafi sai ki dauko kullin nan naki na dankali wanda dama kin hada shi da kayan dandano, ki zuba dai dai yadda girman kofin wainar yake, sai ki bar shi kasan ya soyu ya yi ja, sannan ki juya idan kika juya ki ka ga bai yi ja ba za ki iya mai da shi.

Amma fa a hankali za ki yi abin, don ka da ya barbaje saboda ba shinkafa ba ce balanta ta yi karfi, bayan nan sai ki sauke inda ki ka juya shi ma idan ya yi ja sai ki kwashe ta. Shi kenan uwargida kin gama hada masar dankali a ci dadi lafiya

 

Ana ci da miyar jajjage;

 

Abubuwan da uwargida za ta tanada:

 

Mai, Koran Tattasai, Albasa, kwai, Magi.

 

Za ki zuba mai a abin suyarki ki yanka albasa da da koran tattasanki sannan sai ki jajjaga attarugun, bayan kin gama shi ma sai ki zuba shi a ciki sai ki zuba magi, idan suka soyu sai ki fasa kwai kamar biyu haka ki zuba a ciki ki rufe ki barshi ya yi kamar dakika 30 ko 40, sai ki bude ki juya, amma kada ki cika magi da yawa daya ma ya isa sai ki ci wainarki ta dan kwali da shi idan kuma baki da kayan yin miyar jajjage za ki iya ci da yaji.

 

 

 

Yadda Ake Awara

Sana’ar Awara sana’a ce mai kyau, kuma ana samu sosai, sannan kuma tana da riba sosai, waken da ake amfani da shi gun sarrafa Awara na da amfani a jikin dan’adam, Awara dai ana yin ta ne da waken soya.

Abubuwan da za ki tanada su ne;

Waken soya, Man gyada, Ruwan tsami ko Alum, Albasa, Tattasai, Magi fari, Gishiri, Abin tacewa da kuma Yaji.

Yadda ake hada Awara:

Da farko za ki samu wakenki na soya, sai ki gyara shi, sannan ki jika shi a ruwa, ruwan ya sha kansa, sannan sai ki rufe ki barshi ya kwana daya, idan ya kwana sannan ya jiku za ki ga ya yi manya-manya shi ne ya jiku, sannan ki wanke shi idan da tsakuwa sai ki rege shi. Yadda za ki rede shi ne, za ki samu kwarya ko wata roba ‘yar babba haka mai dan girma, sai ki zuba shi a cikinta ki sa masa ruwa ya sha kansa sannan ki samu wata robar kamarta ko wadda ta fi ta, daga nan sai ki diga masa ruwan tsami kina jijjigawa, kina zubawa tare da ruwan cikin tafasarwa da babu komai a ciki kina zubawa, idan ruwan ya kare sai ki dauko tafasar ki zuba iya ruwan kadan ban da waken da ya zuba a cikinta.

Sannan sai ki sake daga wadda kika daga sama ki sake jijjigawa kina zuba waken tare da ruwan idan ruwan ya kare ki sake mai da shi haka za ki yi ta yi har waken ya zube cikin dayar za ki ga tsakuwar gaba daya ta kwanta a kasa, sai ki sake dauraye shi ki kai nika idan aka nika shi ya yi laushi sai ki dauko abin tacewa ki sa masa ruwa a cikin kullin sosai kamar yadda a ke tace kullin kamu, sai ki tace shi haka, idan kika gama tacewa sai ki samu tukunyar da za ta dauke, sannan ruwan kullin, sai ki zuba shi cikin tukunya ki dora shi a wuta ki zuba masa gishiri da farin magi yadda zai ji da dan jajjagen tattasai ki zuba a ciki ki yanka albasa kanana ki zuba ciki sai ki rufe tukunya ki barta har sai ta fara tafasa idan ta fara tafasa sai ki dauko wannan ruwan tsamin kina dan zubawa da kadan da kadan tana tafasa kina zubawa za ki ga tana haduwa tana kama jikinta ta na komawa waje daya kina yin haka, ita kuma tana komawa gefe har sai kin ga gaba dayanta ta koma gefe.

shi kuma ruwan ya zama kalar ruwa zallah bashi da hadi da wani gari gari, sannan sai ki tanadi abun tacewa ki shimfida shi cikin wani baho haka sai ki dauko wannan tukunyar sai ki zube ta ciki za ki ga ta tace ruwan gaba daya ya koma ruwa a bahon cikin abin tatar kuma Awarar, sai ki dauko abin tatar tare da Awarar ki cire su a cikin ruwan sai ki yi kokari ki matse sosai yadda ruwan zai tsane idan ba za ki iya matsewa ba sai ki rataye, tun ruwan yana zuba har sai ya tsane gaba daya sannan ki bude shi ki yayyanka shi a tsaitsaye sannan ki yanka ta a kwance kamar sikari gudaji kanana yadda za ki soya sai ki zuba masa mai da yawa yadda idan za’a yi tuya ake zubawa sannan ki dora shi a wuta ki dan sa masa albasa saboda ya yi kamshi idan ya yi zafi ki fara zuba Awaran cikin mai yadda za ta soyu,idan ta yi kalar kasa-kasa sai ki juya ta idan ya yi kalar kasa shi kenan sai ki sauke taki barbada mata yaji idan me son yaji, ce sai ci kawai.

Exit mobile version