Kamar kullum yau kuma Na shirya tsab don in kawo muku kala kalan miyoyi, domin Uwargida ta sauyawa megida miya. Duk da cewar na San mu mata iyayen gida muna da matukar kokarin ganin muna kyautatawa megida wajen armasa girkin mu ta yadda duk Inda ya je yana tunanin yau kuma wane salon GIRKI zai zo ya Tarar a gida. Kadda in cika Ku da surutu, bari mu tsunduma kan abinda ya hadamu a dakin girkin.
MIYAR EGUSI
Kayan hadi
2- Bushashshen Kifi
3- Stock fish (kifin kwalla)
4- markadaddun kayan miya
5- Crayfish (nikakke)
6- Nama
7- Sinadarin dandano
8- Gishiri
10-Obeshe (wata daddawa ce, ta yare)
11-Albasa
12-Ugu ko Shuwaka
13-Kayan kamshi
Yadda A Ke Hadi
Da farko Uwargida za ki wanke namanki ki zuba a tukunya, Sai a wanke bushashshen kifi ki cire kayoyin ki gyara shi sosai.kisa gishiri kadan a gurin wankewar. Sai ki zuba a cikin tukunyar da ki ka zuba naman. Sai ki wanke stock fish din ki da ruwan dumi da gishiri. Ki wanke sosai ki gyara shi, sai ki zuba a cikin tukunyar da kika zuba nama da bushashshen kifin.sai duk a hadasu a tukunya daya a Dora a wuta. A zuba sinadarin dandano da kayan kamshi da Albasa, a dora a wuta a dafasu su dahu. In ki ka dafa su suka dahu sai ki sauke ki tace ruwan ki kuma tsince Naman guri daya sai ki soya shi, amma ba lallai ba ne sai an soya zaki iya barin shi haka. Sai uwar gida ta maida tukunyarta a wuta ta zuba man ja. Ta kawo markadanta ta zuba sai ta soya markadan idan ya soyu sai ta kawo ruwan nan da ta yi tafasar nama da kifi ta zuba. Sai ta zuba sinadarin girki da gishiri, yana da kyau uwargida ta kula don kada ta cika. Kada ki manta dama kin sa su a ruwan tafasar. Amma in ya wadarar ma ba sai sai an kara ba. Sai ki kawo daddawar nan wato obeshe ki zuba ki barshi su Dan dahu sai ki Dan zuba ruwan kana kadan. Ki zuba tafashashshen nama da kifayen, ki kawo dakakken cryfish ki zuba. Kafin ya dan kara dahuwa sai ki dauko Albasa ki yankata mitsi mitsi, ki kawo egusin ki ki zuba a can kwano ki zuba Albasar a kai. Ki sa ruwa ki kwa6a da dan tauri kamar kwaa6in danwake dama ruwan miyarki ya gama dahuwa sai ki ringa saka egusin nan kamar sakin danwake in kika gama sai ki barshi ya dahu, za ki ga miyarki ta yi kamar miyar kwai. Sai a kawo wankakken ganyan Shuwaka a zuba, ko ganyen ugu. Duk dai Wanda mutum ya ke so. A bada ‘yan mintina sai a sauke. Za a iya ci da sakwara, ko Tuwan shinkafa, ko semo. Kada uwargida ta manta da kwanon maigida ya zama shine Na farko.