Hakika girki ba karamar martaba ya ke karawa ’ya mace ba. Wannan ya sa mu ka ware fili na musamman, domin koya wa mata girki iri-iri; kama daga na zamani har zuwa na gargajiya.
WAINAR SAMOBITA
Kayan Hadi:
1-Garin Samobita
3-Yis
4-Baking powder
5-Gishiri
6-Sinadarin dandano
7-Attaruhu
8-Albasa
9-koren tattasai
11-Thyme
12- Dwai
Yadda A Ke HadAwa
Da farko uwargida, idan ta tanadi wadannan abubuwan sai ta sami mazubi mai kyau, ta dauki rariyarta ta tankade garin Samobitanta a ciki. Ta zuba yis da baking pawder dan kadan. Sai ta dauki attaruhunta da albasarta ta wanke su ta tsaftace su, kana ta jajjaga su, ta zuba a cikin garin Samobita.
Sai kuma ta dauki koren tattasanta ta wanke shi, ta yayyanka shi kanana. Sai ta zuba a cikin garin Samobitan. Sai ta zuba gishiri, sindarin dandano, curry da thyme. Sai ta juya sosai har su hade jikinsu sosai. Ta zuba rowan dumi ta dama shi, kamar yadda za ta dama kullin wainar shinkafa.
Sai kuma ta sami mazubi ta fasa kwai, ta kada shi sosai, sannan sai ta zuba a cikin kullin. Sai ta saka shi a rana har ya kumburo. Sai ta zo ta dauki kaskon suyar wainar shinkafa ta na diga ma sa ta na soyawa.
A ringa bari ya na soyuwa sosai har cikinsa, kafin a juya. Idan ta soyu za ta rika fitar da wani kamshi mai dadi.
Sai a sami mazubi mai kyau a zuba wa maigida da sauran mutanen gida. Za a iya cin sa haka ko a ci da miyar alayyahu.