Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Girma Ya Fadi Rakumi Da Sha Ruwan ’Yan Tsaki

by
4 months ago
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Girma Ya Fadi Rakumi Da Sha Ruwan ’Yan Tsaki
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Yau Ake Cika Shekaru Hudu Da Kafa Kwamitin Kula Da Harkokin Waje Na Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin

Kasashen BRICS Sun Yi Kira A Hada Kai Don Tinkarar Sauyin Yanayi

Daga CRI Hausa,

Duk da irin kumfar baki da ta da jijiyar wuya da kasar Amurka ke yi na neman karfin fada a ji a duniya, musamman wajen neman juya akalar duniyar yadda take so, amma abin takaici ne yadda take bayyana gazawarta a fili. Alal misali a karshen makon da ya gabata jakadan kasar Sin a MDD ya yi tsokaci game da takardar bayanan da ofishin wakiliyar Amurka ta gabatarwa MDD, wakilin kasar Sin ya bayyana a karshen mako cewa, abin dariya ne yadda ofishin wakiliyar Amurka ya bayyana yunkurin lalata tasirin kasar Sin a matsayin nasarar da kasar ta cimma har ma ta fito gaban duniya tana wannan ikirarin. Wannan dai ya yi kama da wasan yara, ko kuma abin da masu hikimar magana ke cewa, “Abin dariya wai yara sun tsinci hakori.”
A ranar Alhamis ne dai ofishin wakiliyar kasar Amurka ya wallafa a shafinsa na intanet wata takardar bayanai a gaban MDD mai taken “Mayar da shugabancin Amurka a MDD a matsayin nasarar da shugaba Biden ya cimma cikin shekara guda,” inda aka gabatar da zarge-zarge marasa tushe kan kasar Sin. A martanin da ya mayar kan tambayoyin da ’yan jarida suka yi masa, Zhang Jun, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya bayyana irin rashin hikimomin dake kunshe cikin takardar bayanan da ofishin wakiliyar Amurka ya gabatar, inda ya bayyana cewa, abin kunya ne, kuma lamarin ya wuce hankali a ce Amurka tana lissafa neman dakile tasirin kasar Sin a gaban MDD a matsayin wani muhimmin aiki ko kuma a matsayin babbar nasarar da ta cimma. Zhang ya ce, gudunmawar da kasar Sin ta bayar ga zaman lafiya da cigaban duniya, da irin goyon bayan da take baiwa MDD da kuma taimakon da take baiwa sauran kasashen duniya suna da matukar muhimmanci kuma kowa yana kallon yadda lamurran suke faruwa. Abin da kasar Sin take bukata shi ne yin hadin gwiwar moriyar juna maimakon yin baba-kere, da tabbatar da daidaito maimakon yin zalunci, da gudanar da al’amurra a bayyane gami da shigar da kowane bangare maimakon kafa shinge da yin shamaki, da kuma tabbatar da zaman lafiya maimakon neman tada husuma da yin fito-na-fito. Game da yadda Amurka take kokarin bata sunan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun yanayin hakkin dan adam a yankin Xinjiang, Zhang ya ce, gaskiyar magana shi ne, yankin Xinjiang yana cin moriyar zaman lafiya, da samun bunkasuwa. Rayuwar Sinawa tana kara kyautata a kullum. Hakika wannan lamari ya yi kama da abin da masu hikimar magana ke cewa, “Girma ya fadi wai rakumi da shan ruwa ’yan tsaki.” Maimakon Amurka ta mayar da hankali wajen neman daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa, sai ta buge da batun tunanin yin fito-na-fito da neman lalata tasirin kasar Sin da sauran kasashe, wanda yin hakan babbar matsala ce dake haifar da koma baya ga hadin kai da amincewa da juna a tsakanin mambobin kasashe, haka kuma wannan mataki zai iya yin kafar ungulu tare da haifar da cikas ga ayyukan MDD. (Ahmad Fagam)

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Lokaci Ya Yi Da ‘Yan Siyasar Lithuania Masu Tada Hankali Za Su Farka

Next Post

Filayen Jiragen Saman Kasar Sin Sun Samu Karuwar Fasinjoji A Bara

Labarai Masu Nasaba

Yau Ake Cika Shekaru Hudu Da Kafa Kwamitin Kula Da Harkokin Waje Na Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin

Yau Ake Cika Shekaru Hudu Da Kafa Kwamitin Kula Da Harkokin Waje Na Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin

by CMG Hausa
17 hours ago
0

...

Kasashen BRICS Sun Yi Kira A Hada Kai Don Tinkarar Sauyin Yanayi

Kasashen BRICS Sun Yi Kira A Hada Kai Don Tinkarar Sauyin Yanayi

by CMG Hausa
17 hours ago
0

...

Al’ummar Afirka Ba Su Bukatar A Yi Musu Lacca

Al’ummar Afirka Ba Su Bukatar A Yi Musu Lacca

by CMG Hausa
20 hours ago
0

...

Masana sun yi Allah wadai da yunkurin Amurka na neman dakile cigaban al’ummar Xinjiang

Masana sun yi Allah wadai da yunkurin Amurka na neman dakile cigaban al’ummar Xinjiang

by CMG Hausa
20 hours ago
0

...

Next Post
Filayen Jiragen Saman Kasar Sin Sun Samu Karuwar Fasinjoji A Bara

Filayen Jiragen Saman Kasar Sin Sun Samu Karuwar Fasinjoji A Bara

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: