Tattaunawar WAKILINMU MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da Furodusa Yunusa Mu’azu Na MASANA’ANTAR KANNYWOOD.
Da Farko Za Mu So Mu Ji Cikakken Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.
To ni dai sunana Yunusa Mu’azu, an haife ni ne a Jihar Gombe. Na yi karatuna na Firamare da Sakandire duka a Jihar Gombe.To daga nan sai na dawo nan Jihar Kano kuma na shiga cikin harkar fina-finai. To bayan na fara harkar fina-finai sai na kara komawa makaranta na je na yi (Diploma) a (Purchasing and Supply) daga shekarar 2010 zuwa 2012. Sannan na kara yin wata (Diploma) din a Film and Telebision Production, a Northwest Unibersity wadda a ka fi sani da Jami’ar Yusuf Maitama Sule a yanzu.
Ya Ya A Ka Yi Ka Samu Kanka A Cikin Masana’antar Fina-finai?
A Wanne Lokaci Ne Ka Fara Aiki A wannan Masana’antar?
Eh to na dade ina tare da masana’antar fina-finai, amma da fara aiki a cikin masana’antar na fara ne a shekarar 2009. To tun daga wannan lokacin ga shi Allah ya na taimakawa tun daga mataki na kasa ga shi a na ta kara yo sama.
A Lokacin Da A Ka Gabatar Maka Da Wannan Aiki Na Farko Da Ka Fara Yi A Kaduna, Wane Irin Kalubale Ka Fuskanta Duba Da Cewa Shi ne Aikinka Na Farko A Cikin Masana’antar?
To gaskiya ban fuskanci kalubale ba da yawa, saboda a lokacin nasan aikin tunda ina taya shi danuwana tun a baya. Kuma mafi yawan wadanda mu ka yi aikin tare da su a lokacin duk na san su sun san ni, to sun taimaka min sosai wajen ganin samun nasarar aikin. To a haka dai na yi wannan aikin cikin nasara kuma kowa ya yaba wannan aikin nawa. To tun daga wannan aikin ne fa a ka fara ahh daman wane ya iya aiki haka, to shi ne fa sai na ci-gaba da samun aiki daga bangarori daban-daban. A sanadin haka, kusan gaskiya duk wani fitaccen mai bada umarni a wannan masana’anta wato Darakta na yi aiki da shi a wannan lokaci.
Duk Wanda Ya San Yunusa Mu’azu A Masana’antar Fina-finai, Kusan Ya Sanka Ne A Matsayin Mai Shiryawa Da Kuma Bada Umarni A Cikin Masana’antar, Ya Ya A Ka Yi Ka Fara Shirya Fina-finai Da Kuma Bada Umarni?
To Kamar Yadda na fada dazu, farko dai na fara yin aikin (continuity) ne wato mai kula da ci-gaban shiri, amma daga baya na fara shirya fina-finai. Kuma fim na farko da na shirya fim dina ne, sai danuwana shi ma ya bani fim dinsa na shirya duba da yadda ya yaba wannan fim din nawa da na shirya. To daga nan ne na ci-gaba da shirya fina-finai kuma na mutane daban-daban. To amma duk da haka na fi bada karfi a (continuity) saboda shi na fi iyawa kuma shi na fi so ma a raina a lokacin. To daga nan ina ta yi, sai wasu daga cikin daraktocin su ke bani shawarar cewa ai nima zan iya ba da umarni a cikin fim, tun duk kowa nasan yadda ya ke aiki, kuma na je makaranta na kara sanin abun a ilimance. To bayan na gama makaranta na ba da umarni a cikin wani fim guda daya mai suna “Lantana” daga shi kuma na zo na yi fim din “Ka Yi Min Uzuri”, to zuwa yanzu dai fina-finai guda uku ne na fito a matsayin mai bada umarni a cikinsu.
To Wanne Ne Fim Dinka Na Farko Da Ka Fara Shiryawa?
Duba Da Cewa Wannan Fim Na Matar Hamza Shi Ne Fim Na Farko Da Ka Fara Shiryawa A Cikin Wannan Masana’anta, Wane Irin Kalubale Ka Fuskanta A Lokacin Da Ka Ke Shirya Wannan Fim Din, Ko Tunda Daman Ka Na Da Kwarewa A Cikin Harkar Ba Ka Samu Wani Kalubale Ba?
Ai ba zai taba yiwuwa ka yi fim ka ce ka yi shi cikin nasara dari bisa dari ba, dole ne za a dan samu ‘yan matsaloli nan-da-chan. Wani lokacin za ka dan samu kalubale daga abokan aikinka, ko wani abu makamancin haka. Amma lokacin duk da fim dina ne na farko, amma da ya ke ina zaune da kowa lafiya ban samu wata matsala da jarumaina ko wasu daga cikin abokan aikina ba. Amma dai an dan samu kalubale kadan, saboda na sha wahala sosai a lokacin aikin fim din, don wani lokacin ko bacci ba na iya yi a lokacin da mu ke aikin fim din.
A Tsahon Shekarun Da Ka Dauka Ka Na Aiki A Wannan Masana’anta Ta Kannywood, Izuwa Yanzu Fina-finan Da Ka Shirya Sun Kai Kamar Guda Nawa?
Eh to gaskiya na shirya fina-finai sun kai kamar guda goma sha biyu haka. Sannan kuma na bada umarni a cikin fina-finai guda uku. Wannan shi ne a takaice.
To A Cikin Wadannan Fina-finan Da Ka Yi A Tsahon Wannan Lokaci, Wanne Fim Ne Ka Fi So A Cikinsu, Wanda Duk Lokacin Da Ka Tuna Da Shi Ka Ke Jin Dadi Kuma Ka Ke Alfaharin Cewa Kai Ne Ka Yi Shi?