Akalla daliban wata makarantar Islamiyya 22 da suka hada da malamai biyu sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a dakin kwanansu da ke tsakiyar birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.
Rahotanni sun ce, masu aikin kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar wadda ta tashi da safiyar a Darul Kuran Ittifakiyyah, in da dalibai ke hadda Al-Kur’ani, yayin da hukumomin kasar suka bayyana gobarar a matsayin mafi muni da aka gani cikin shekaru 20.
Ministan ilimi Tengku Adnan Tengku Mansor ya ce, rashin hanyoyin fita daga dakin kwana daliban ya taimaka wajen mutuwarsu.
Shugaban ‘yan sandan birnin Amar Singh ya ce sun samu gawarwakin daliban menne da juna.
Kashi 60 na al’ummar Malaysia mai yawan mutane miliyan 30 Musulmai ne.