Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi
Rahotanin da garin Birnin-kebbi na bayyana cewa an samu tashin wata gobara da ta rushe makarantar firamare da ke ungwar Gudi a jiya a cikin tsohon garin Birnin-kebbi.
Wutar dai ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:35 na daren Asabar, inda dai har zuwa lokacin da wakilinmu ya haɗa wannan rahoton ba a san musababin tashin wutar ba.
Kamar yadda rahotanni daga unguwar ta Gudi ke nuna cewa, wannan tashin wutar ne karo na biyu a wannan makarantar ta Gudi.
Domin jin ɓangaren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar kebbi, wakilinmu ya samu zantawa da Shugaban hukumar ta SEMA, Alhaji Sani Dododo inda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ci gaba da cewa; “na kira daraktan ‘yan kwana-kwana, Alhaji Bello Zagga inda a nan take jami’an hukumar suka iso makarantar domin bada nasu gudummawa ta hanyar kashe wutar.
“Za mu binciki musabbabin tashin ita wutar a wannan makarantar ta unguwar Hudu dake cikin tsohon garin Birnin-kebbi”. Inji shi
Ya ƙara da cewa, ba a samu asarar rai ko guda a wannan gobara ba.
Wutar dai ta lashe layin azuzuwa guda ɗaya da ofishin baturen makarantar sai kuma azuzuwa guda biyu duk wutar ta cinye su.