Gobara Ta Ci Rayukan Mutum Uku A Zamfara

A daren jiya ne al’ummar Filin Jirgi na Karamar Hukumar Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, suka shiga cikin firgici da ban tausayi, sakamakon Gobara da ta tashi a Gidan Malam Sani Jibril Ma’aikaci a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara, Inda ta yi sanadiyyar Rasuwar ‘Ya’yansa uku.

Sani Jibril, ya bayyana ma wakilinmu cewa,  ‘ Wannan Gobara abu ce mukaddari daga Allah, don a dakin da wutar ta fara ci babu wani abin konawa a ciki ko da maganin Sauro. Kuma babu wuta balle ayi zaton cewa ita ce sanadi. Wannan abu kaddara ce daga Allah, kuma jarabawa ce da yake jarabtar bayinsa.

Malam Sani, ya kara da cewa, Allah Ya azurtani da ‘Ya ‘ya Bakwai, yanzu haka ya amshi hudu a lokaci guda. Cikin wadanda suka rasu daga ciki sun hada da, Zainab, ‘Yar shekaru bakwai, sai Rabi’atu ‘yar shekaru sha biyu da kuma danbaba mai shekaru uku. Duk wadannan Yara nawa, sun rasu a sakamakon wannan Gobara. Kuma yanzu haka ga Gidan nawa ya kone kurmus don babu abin da aka fidda.

Roko na ga Allah Ya amshi wadanna Yara nawa Shahidai. Kuma Ya albarkaci wadanda ya bar mana, amin.

Kuma ina mika godiya ta ga Makwabtana da Jami’an kashe Gobara don sun taimaka mani daidai gwargawdo, Allah Ya saka da alherinSa amin.

Exit mobile version