Munkaila Abdullah" />

Gobara Ta Cinye Gidan Babban Akantan Jihar Jigawa

A jiya ne wata mummunar gobara ta kama tareda kone gidan Akantan jihar Jigawa

Alhaji Haruna Ahmed Aminu wadda ke Dutse babban birnin jihar.

Wannan gobara wadda ta afku da tsakar rana a jiya talata ana zargin ta tashi ne sakamakon wutar lantarki wadda aka dauke ta a daren litinin sakamakon iskar hadari da ta taso kuma tayi sanadiyyar lalacewar kayayyakin lantarkin.

Wani daga cikin wadanda al’amarin ya afku kan idonsa ya bayyanawa wakilinmu cewa a lokacin da aka dawo wutar lantarkin shi ne da hannunsa ya sauya layin daga injin janareto zuwa wutar lantarkin.

Haka kuma ya karada cewa, bayan sauya layin tun safe sai can da rana yaji wani ya fito daga gidan yana ihun neman dauki cewa wuta ta kama cikin gidan.

“A lokacin da aka dawo da wutar lantarkin da misalin karfe 12:00 na rana ni ne na sauya layin daga janareto zuwa wutar lantarki ta NEPA”

“Bayan dan wani lokaci kawai sai ga wani ya fito daga cikin gidan yana ihun neman dauki cewa wuta! Wuta!! Yana yunkurin neman ruwa domin ya diba”

Haka kuma ya bayyanawa majiyarmu cewa bisa dukkan alamu wutar ta fara ne daga dakin kwanciya na Akantar yadda daga bisani ta tsallaka sauran wurare a gidan.

Daga karshe an yi nasarar kashe gobarar tareda daukin al’umma makwabta da kuma fannin kashe gobara na filin jirgin sama dake Dutse.

Exit mobile version