Connect with us

Nahiyar Afirka

Gobara Ta Cinye Gidan Tarihi Mai Shekara 200 A Brazil

Published

on

Wata mummunar gobara ta cinye gidan ajiyen kayayyakin tarihi na Brazil da aka kafa shekaru 200 da suka gabata a birnin Rio de Janeiro.
Jami’an kashe gobara na ci gaba da kokarin kawar da wutar a gidan tarihin mai dauke da nau’ukan kayayyaki daban-daban sama da Miliyan 20.
Shugaban kasar, Michel Temer a wani sakon Twitter ya bayyana bakin cikinsa da aukuwar ibtila’in wanda ya salwantar da ayyukan bincike da ilimi na tsawon shekaru 200.
Kawo yanzu babu rahoto game da wadanda suka samu rauni sakamakon gobarar wadda ta tashi a yammacin Lahadi.
Kafafen talabijin na kasar sun nuna yadda gobarar ta mamaye daukacin ginin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: