Rundunar ‘yan sanda kasar Uganda ta tabbatar da afkuwar wata gobara da ta yi sanadiyyar mutuwar wasu yara ‘yan makaranta su tara, gobarar ta tashi ne a dakin kwanan daliban a wata makaranta da ke kudu masu yammacin kasar ta Uganda, a yau Litinin.
An kama wasu dalibai da ake zargin sune suka kona wutar, daliban wadanda ba a dade da korar su ba daga makarantar, sune ake zargin sun cinna wutar saboda jin zafin abinda aka musu, ana yawan samun aikata laifukka a makarantun sakandiren yankin kasar.
Duk da har yanzu hukumar ‘yan sandan yankin ta ce, tana kan gudanar da bincika don tabbatar da gaskiyar abinda ya kawo wutar, akwai rahotannin da suke cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai dalibai 20, sabannin tara da ake ta fada.