Khalid Idris Doya" />

Gobara Ta Hallaka Mutane Shida A Kano

Mutane shida ne suka mutu a safiyar jiya Asabar a sanadiyyar aukuwar Gobara wacce ta tashi a wani gida da ke layin sabuwar unguwar Hausawa Kuarters da ke karamar hukumar Tarauni a cikin jihar Kano.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga majiyarmu, Kakakin Rundunar ‘yan Sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya shaida cewar daga cikin wadanda gobaran ta rutsa da su, har da mahaifinsu da kuma ‘ya’yansa guda uku da suke cikin gidan a lokacin da wutar ta tashi.
Abdullahi ya bayyana ceear an samu rahoton aukuwar lamarin ne da karfe 3:30 na Asubayi, inda ya shaida cewar ‘yan sanda sun yi kokorin zuwa wajen domin bayar da agaji, dukkanin mutane shida da suke gidan wutar ta hallakasu.
Ya kara da cewa da hadin guiwar jami’an ‘yan sanda da hukumar ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar.
Ya shaida cewar har zuwa yanzu basu kai ga gano mubabbin tashin gobatar da kuma iyaka asarar da ya yi ba, Amma da zarar suka tantance komai za su bayyana ga manema labaru.
Sai dai ya bayyana cewar sun iya gano cewar wutar ta fara cine tun daga cikin daki har ta mamaye gidan gaba daya, wanda hakan ya hana wadanda suke ciki samun damar kubuta.

Exit mobile version