Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

 

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,

 

Mummunar gobara maras misaltuwa ta yi gagarumar barna a Babbar Kasuwar Sakkwato wadda ta zama sanadiyar hasarar dimbin dukiya da kudi na biliyoyin naira.

Gobarar wadda ta fara ci tun misalin karfe hudu na Asuba daga Kofar ‘Yan Roba, ya zuwa yanzu ta ci bangarori da dama na kasuwar.

Wani dan kasuwa Nata’ala Sambo Babi ya bayyana cewar ba a san musabbabin tashin gobarar ba haka ma ba za a iya bayyana dimbin hasarar da aka yi ba, sai dai kawai Allah ya mayar masu da alheri. “A yanzu haka tun kafin gobarar ta kai shagunanmu mun samu nasarar kwashe abin da za mu iya kwashewa, bayan mun kwashe ne gobarar ta kawo ta layin mu har ta wuce gaba. Abin ba a cewa komai sai Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya bayyana.

Tuni Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci Babbar Kasuwar domin gani da idonsa a inda ya bayyana jimami da alhinin dimbin hasarar da ‘yan kasuwa masu neman na kansu suka tafka.

“Wannan gobarar abin bakin ciki ce, Muna iyakar kokari domin ganin mun takaita yawan hasara. Dukkanin jami’an tsaro suna nan tare da mu domin ganin ba a sace kayan jama’a ba, don haka muna kira ga jama’a da su kara hakuri muna iyakar kokari domin ganin mun shawo kan wannan ibtila’in.”

Tuni dai Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa kwamitin musamman domin binciken musabbabin gobarar a karkashin Mataimakin Gwamna, Hon. Manir Muhammad Dan-Iya. Sauran manbobin kwamitin sun hada da shugaban kwamitin Kasuwanci a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Kwamishinan Kasuwanci daKwamishinan Filaye da Gidaje.

Sauran sune wakilin Majalisar Sarkin Musulmi, Babban Daraktan Kasuwar, Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara, Shugaban Hukumar Gudanarwar Kasuwar, Shugaban Cibiyar ‘Yan Kasuwa, Shugaban Kungiyar ‘Yan Tireda, Shugaban Kungiyar ‘Yan Tireda na Kasuwar, Sheik Bello Yabo da Alhaji Namadina Abdulrahman.

Gwamnan ya dorawa kwamitin alhakin bincike musabbabin tashin gobarar, kididdigar hasarar da aka yi da tallafin da ya kamata a bayar, matakan kiyaye sake afkuwar gobarar da sauransu.

Exit mobile version