Akalla shaguna 62 da gine-ginen jama’a ne a karshen mako suka kone kurmus sakamakon barkewar Gobara a kasuwar Ijesha da ke Oshadi a jihar Legas.
Wutar Gobarar an ce ta fara tashi ne da karshe biyar na yammaci har zuwa 8:50 tana ci gaba da falfaluwa, lamarin da ya shafi shaguna 62 da gidaje sama da 28.
A cewar Ko’odinetan shiyyar kudu maso yamma na hukumar samar da agajin gaggawa (SEMA), Mista Ibrahim Farinloye, ya shaida cewar, “Wutar ana tsammanin ya tashi ne daga wani daki, inda ya fantsama zuwa zuwa shago a yayin da abun dafa abinci da gas ke kunne, lamarin da ya kai ga barkewar wutar falfal.”
Ya kuma ce, an samu nasarar kashe gobarar bayan daukan awanni, kana ba a yi asarar rayuka ko jikkatan jama’a sakamkon wannan lamarin ba, sai dai ya ce an yi asarar miliyoyin naira na dukiya da kaddara.
Jami’in ya shaida cewar jinkirin kashe wutar ya samu asali ne sakamakon rashin ruwa a kusa da inda lamarin ya faru, yana mai cewa sai da aka je wuri mai nisa ake samun ruwan da aka kashe wutar da shi.
Ya ce, za su duba irin asarar da aka yi domin ganin hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen taimakawa ga wadanda lamarin ya shafa domin rage musu radadi.
APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbin Dan Majalisa A Jigawa
Daga Munkaila Abdullah, Hukumar zabe ta INEC ta bayyana Jam'iyya...