Daga Jamil Gulma,
Wata gobara da ta tashi tsakiyar daren jiya Lahadi sanadiyyar bugawar wata transfoma da ke bakin babbar kasuwar Argungu da ke jihar Kebbi ta lakume shaguna da kuma rumfunan masu sayarda kayangwari wanda ya yi sanadiyyar hasarar milliyoyin nairori.
Daya daga cikin wadanda shagunansu suka money Alhaji Ibrahim Samaila (Aguro) wanda ke da shagon sayarda wayar salula ya bayyanawa wakilinmu da cewa an kira shi ne da misalign karfe daya da rabi na dare sai daya daga cikin yan uwansa ya kira shi ta wayar matarsa sanadiyyar lalacewar layin sa ya gaya shagon sa ya kama wuta.
Lokacin da ya isa wajen ya fatar shagon ba wajen shiga duo da ya ke jama’a sun taru ana ta famar kashe wutar, da ya ke wutar ta ruru sosai ba wanda ke iya shiga kwantenar don fitowa da wadansu kaya saboda haka shagon sa ba abinda aka fitar. Ya ce ya yi hasarar dukiyar da za ta kai kimanin naira milliyan biyar ko fiye.
Ya kuma kara da cewa daman sun dade suka samum barazana daga wannan transfoma saboda sau da yawa ta kan buga sai wuta ta rinka watsi har sai mutane sun watse sannan daga baya jami’an ma’aikatar wuta su zo su gyara, amma dai ba a taba samun irin wannan ba.
Shagunan da suka kone akwai shagon sayarda wayar salula, shagon sayarda kananan tufafi da kayan wasanni mallakar Alfa, shagon Malam Habibu mai sayarda roba, da kuma rumfunan masu sayarda kayangwari sai dai ba rahoton salwantar rayuwa.
Wakilinmu nemi jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar samarwa da kuma raba wutar lantarki ta Kaduna Malam Idris Muhammed amma dai ya ce har wannan lokacin ba su sami wani rahoto ba daga Argungu, sai dai ya ce daman sai jami’an na su sun kammala tattara bayanai kafin su kawo rahoton afkuwar irin wannan lamarin. Ya kuma bayarda tabbacin hukumar za ta yi gaggawar daukar matakan da suka dace don farantawa rayuwar masu huldar da su.
Tuni jami’an kamfanin samarda wutar lantarki da kuma rabawa na Kaduna (KEDCO) sun dukufa wajen gyara transfomar da abin ya faru.
Al’ummar jihar dai suna kokawa kan rashin motocin kashe gobara wanda yanzu haka a karamar hukumar mulki ta Dandi kawai ke da mota daya da shugaban karamar hukumar mulkin ya gyara.