Connect with us

LABARAI

Gobara Ta Lashe Babbar Kasuwar Azare

Published

on

A wani sabon ibtila’in da ya sake barkewa a jihar Bauchi, wata mummunar Gobara ta cinye babban kasuwar karamar hukumar Azare da ke jihar Bauchi kacukam. lamarin da ya sabbaba asaran miliyoyin naira da kuma salwantar kayyakin saidawa na jama’an karamar hukukar.
Wannan ibtila’in ta auku ne a daren ranar Lahadi inda lamarin ta kai ga tayar da hankulan jama’an garin. Wakilinmu ya labarto cewar ita Azare dai ita ce babbar karamar hukuma mafi girma a dukkanin kananan hukumomin da suke jihar Bauchi, kana ita wannan babban kasuwar wato ‘Central Market Azare’ ita ce kasuwa daya tilau da ake hada-hadan kasuwanci a cikinta a wannan yankin.
Gobarar wacce take zuwa kwana guda bayan da wata mummunar Guguwa ta yi mummunar ta’adi wa illahirin jama’an da suke cikin garin na Bauchi, kama daga fadar jihar da kuma wasu kananan hukumomin, inda kuma a ranar Lahadi sai ga wannan sabon zancen.
Wakilinmu ya tuntibi wadanda lamarin ya shafa a garin na Azare, inda suka bayyana lamarin a matsayin mummunar musifa. Idris Ibrahim Azare ya shaida mana yadda ta kaya, “Lamarin sai dai mu daga hanu mu gode wa Allah, ita wannan kasuwar ta Central Market daman ita ce babbar kasuwar da ake saye da sayarwa a cikinta. Wutar ta fara tashi ne da misalin karfe sha biyu 12 na daren ranar Lahadi wacce ta kai har zuwa ranar Litinin da Asubayi tana ci gaba da ci,”
“Wutar ta fara tashi ne daga farkon kasuwar, daga nan ta nutsa ta mika cikin tsakiyar kasuwa inda zuciyar kasuwar take. Dukkanin kasuwar ta kone,” In ji Idris.
Ko yaya yanayin asarar da aka yi? “Subhanalla, Malam an yi asaran kayyakin miliyoyin naira, domin dukkanin wani waje ko shago da ya kira sunansa shago ko yanki a cikin kasuwar nan ya gama konewa kurmus. Akalla shagona sama da dubu biyu 2,000 sun cinye da wutar nan kaf. Ba ma a haka kadai asaran ta tsaya kan kayyakin ba, tsurarin kudade da suka kone a cikin kasuwar nan Allah kadai ya san yawansu.
“Da yake ka san an ci kasuwar sallah tun daga Alhamis, zuwa Juma’a, kuma ka san a ranar Juma’a babu aiki, sannan kuma Asabar babu banki, Lahadi ma babu banki, don haka dukkanin cinikin da ‘yan kasuwa muka yi, dole sai ranar Talata za mu kai kudaden banki, sai kuma ga wannan iftila’in ta auku a daren ranar Lahadi da kudade jama’a a ciki, a zahirance kudaden da aka yi asaran a cikin kasuwar nan zan iya shaida maka da cewar miliyoyi ne kawai, domin kuwa ba a cewa komai,” In ji Idris Azare.
Idris Ibrahim ya kuma kara da cewa babu wani takamaimai dalilin da ya janyo tashin wutar wannan gobarar, illa dai wutar, cinta ya wuce kima, “Gaskiya a hasashen wasu na nuni da cewa wai wutar NEPA ne, amma gaskiya wannan lamarin ya wuce wutar NEPA. An saba samun matsalar wutar NEPA amma ana shawo kansa cikin lokaci, amma wannan, kafin ka ce kwabo sai dai ka ji wani shago ya tashi, kan ka lura ya haura ta can yadda ka san wani abu ake hurgawa, don haka gaskiya babu wani takamaimai dalilin tashin wannan wutar, illa dai wuta ta yi barna sosai,” In ji shi.
Mai bamu rahoton ya bayyana cewar bayan wannan lamarin kuma; an samu masu kekasassun zuciya wadanda suka tafka sata wa jama’a a lokacin da wutar ke ci gaba da hauhuwa, “An saci mashina sama da talati,” In ji shi.
LEADERSHIP A Yau ta kuma zanta da daya daga cikin wadanda suka yi mummunar asara a wannan kasuwar ta Azare mai Suna Mustapha Muhammad Murtala wanda kuma shine Ma’ajin kungiyar matasan kasuwar ya shaida yadda suka riski lamarin, “Ni ina da shago a cikin wannan kasuwar ina saida kayyakin bulawus, ina zaune a gida da misalin karfe sha biyu da rabi na dare ne aka kirani ake shaida min cewar shagonmu ya kama da wuta. Ina zuwa cikin kasuwar, na tarar shagonmu ya rigaya ya kone,”
“Tabbas an yi asaran kudade sosai a cikin kasuwar nan, domin ‘yan kasuwarmu da daman gaske da suka kone a cikin kasuwar,”
“A kiyasi ya bayyana cewar kashi biyu cikin uku na shagonan cikin kasuwar duk sun kone kurmus,” In ji Mustapha.
A daidai lokacin da wakilinmun ke masa tambayoyi, ya shaida cewar a daidai wannan lokacin shugaban riko na karamar hukumar ta Katagum ya shiga kasuwar inda ake nuna masa irin wannan asaran da ta auku a karamar hukumarsa.
Sai dai kawo aiko da rahoton babu wani jawabi ko bayanin da muka samu daga mahukunta a karamar hukumar ko cikin jihar, da zarar muka jiyo za mu sanar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: