Gobara Ta Lashe Shagunan Kafintoci Fiye Da 500 A Sabon Garin Zariya
Daga Isa Abdullahi Gidan bakko, Zariya
A daren jiya Juma’a gobara ta kone kasuwar kafintoci a babbar kasuwar ‘yan katako na Sabon garin Zariya,inda Shagunan kafintoci fiye da guda dari hudu suka kone kurmus,ba tare da an Sami damar fita da wani Abu ko da daya ba.
Wakilinmu da ya ziyarci kasuwar a jiya Juma’a,ya gane wa idonsa yadda kasuwar ta kone,yayin da al’umma da dama ke bayar da gudunmuwa wasu abubuwa da suke da alkka da karfe da ake ganin za su iya zama ma su moruwa.
Ganau ya shaida wa wakilinmu cewar,gobarar ta fara ne da misalin karfe uku zuwa hudu na dare,da ake tunanin gobarar ta samo asali ne daga wutar da ta ke fitowa daga injin jannareta dabwaau kafintoci ke amfani da shi.
Alhaji Suleiman Auta,daya daga cikin manyan ‘yan kasuwa da ke sayar da kayayyakin da kafintoci ke amfani da su wajen aikace – aikacensu na kafinta,a cewarsa ya tafka asar da ba zai iya bayyana wa ba.
Alhaji Suleiman ya kara da cewar, wannan asara da suka Sami kansu a ciki,sun fauwala wa Allah da suke sa ran shi ne kawai zai ma su sakayya na dinbin dukiyoyin da suka rasa a wannan gibara.
Shi ko shugaban kungiyar kafintoci na kasuwar Sabon garin Alhaji Suleiman Yusuf Na Hari Mai Allah,da farko cewa ya yi daukacin runfunan wucin gadin da su ke wannan kasuwa da aka ambata,sun kone,Babu wani abu Mai Kama da kusa da aka cire a sassan kasuwar,ya kara da cewar,duk wani matakin da zai Kare dukiya su daga gobara sun dauka,Amma da ya ke jarabawar Allah Babu inda ba ta shiga,shi ya sa a cewarsa,suka fauwala wa matsalolinsu ga Allah da shi ne kawai zai yi ma su sakayya na asarar da suka tsinci kansu a ciki.
Alhaji Na Hari Mai Allah,ya Kuma yi Kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta karamar hukumar Sabon gari da kuma duk Kuma ma su tallafa wa al’umma,da su kawo ma su dauki, na asarar da ta same su.
A da dai jiya Juma’a,Hakimin Sabon gari,dan Barhin Na Zazzau,Alhaji Ahmed Bashari Aminu,ya ziyarci kasuwar lnda ya jajanta ma su, na gobarar da ta same su a wannan kasuwa,
alhaji Ahmed Bashari Aminu ya yi ma su alkawarin yin duk abin da ya kamata,na ganin sun sami tallafin da ya dace,domin samun saukin matsalar da suka tsinci kansu.
A karshe,shugaban kungiyar Na Hari ya nuna matukar Jin dadinsa,na ziyarar jajen da suka tsinci kan su a ciki.
Hadiza Bala Usman Ta Yi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Dikko Inde
Daga Abdullahi Sheme A ranar juma'ar da ta gabatane shugabar...