Khalid Idris Doya" />

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

Ibtila’in gobara ya ci rayuwar mutum uku daga ciki har da uwa da ‘ya’yanta biyu sakamakon gobarar da ya konesu kurmusu, yayin da kuma mutum hudu suka gamu da munanan raunuka.

Wakilinmu ya nakalto cewa, lamarin wanda ya faru a kauyen Riban Garmu da ke gundumar Dewu a karamar hukumar Kirfi da ke Bauchi.

Mambar majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Kirfi, Hon. Abdulkadir Umar Dewu shi ne ya sanar da hakan yayin da ya kai ziyarar jajantawa ga wadanda lamarin ya shafa a madadin gwamnan jihar Bala Muhammad.

Dan majalisar ya ce, akwai matukar zafi da tashin hankali a ga uwa da ‘ya’yanta na ci da wuta.

Daga nan ya bukaci iyalan wadanda lamarin ya shafa da su dauki dangana kana su sauwala komai ga Allah.

Ya wakilci gwamnan jihar Bala Muhammad wajen bada tallafin dubu dari biyu da hamsin N250,000 ga iyalan mamatan domin rage radadi asarar da gobarar ta jawo musu.

Daga bisani gwamnan ya jajantawa Alheninsa bisa wannan babban rashin da aka yi, tare da addu’ar Allah gafarta wa mamatan ya kuma kiyaye faruwar hakan gaba.

Dewu ya nemi jama’an yankin da su kula da dukkanin ababen da ka iya janyo tashin gobara domin kiyaye faruwar hakan a gaba.

Shugaban al’umman yankin, Malam Muhammadu Riban Garmu, ya nuna godiyarsa a bisa nuna damuwa da gwamnan jihar yayi kan wannan iftila’in da ya samesu, yana mai nuna godiyarsu a hakan.

Ya misalta marigayiyar matar a matsayin mace mai kima da mutunci wacce ta rayuwa cikin son zaman lafiya da kaunar juna a kowani lokaci, yana mai cewa za su cigaba da tunata bisa kyawawan halayenta, sai yayi addu’ar Allah jikanta da gafararsa.

Ganau ya shaida cewar lamarin ya faru ne sakamakon matsalar wutar lantarki, inda ya ce wutar ta kone dakuna hudu gaba daya yayin da wasu mutum hudun da suka gamu da raunuka suke kwance a asibitin Kirfi.

Exit mobile version