Connect with us

MANYAN LABARAI

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Yara Uku A Jihar Nasarawa

Published

on

Wata gobara da ta tashi da asubahin yau, a kauyen Ado dake karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa, ta yi sanadiyyar mutuwar wasu yara kanana su uku dukkansu ‘ya’yan mutum daya.

Shaidun gani da ido sun ce, gobarar ta fara ne da misalin karfe 6:30 na safe, duk da har ya zuwa yanzu ba a kai ga gano menene musabbabin tashin gobarar ba, ba a iya nan gobarar ta tsaya ba, ta cinye gidan kurmus.

Wata mata mai makwabtaka da gidan ce ta fara hango hayaki, sai ta yi ihu ta sanar da mijinta, lokacin da mijin ya kai dauki gidan sai ya samu mutanen gidan basa nan, sai ya lura akwai yara a dakin wanda kuma yake a kulle, sunyi ta kokarin balle kofa don ceto yaran amma, haka ya ci tura.

Yaran wanda mahaifinsu Mista Sunday ya bada sunayensu kamar haka, Chimobi shekaru uku, Chinonso shekaru biyar, sai Destiny mai shekaru takwas.

Mista Sunday ya ce: lallai wannan gobarar ta daure musu kai sosai, saboda babu wutar lantarki, sannan ba sa yin girki a daki, suna da kicin inda nan suke yin girkinsu, kuma mata ta fita waje don siyo katin waya, babu wanda ya isa ya fada maka menene musabbabin tashin wannan gobarar.
Advertisement

labarai