Gobarar Makaranta: Gwamnatin Kogi Ta Wanke Makiyaya

Kogi

Daga Ahmed Muh’d Danasabe,

Gwamnatin Jihar Kogi a karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello, ta ce, ko kadan Fulani makiyaya dake zaune a jihar ba su da hannu a kona makarantar sakandiren gwamnati ta GSS Iluke dake yankin karamar hukumar Kabba Bunu a jihar.

Wata sanarwa da ta fito daga Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar, Mista Kingsley Fanwo, ta kuma ce, gwamnatin jihar ta damu matuka gaya game da bankawa makarantar wuta.

“Gwamnatin jihar ta nuna rashin jin dadinta ganin yadda aka yi gaggawar yanke hukuncin cewa Fulani makiyaya ne suka kona wani bangare ko sashen makarantar. Wannan yanke hukuncin da ba a tabbatar da shi ba kuma dargin yana iya tayar da zaune tsaye a jihar.

“Binckenmu ya yi nuni da cewa, gobarar ta afku ne a sakamakon kona jeji babu gaira babu dalili da wasu da ba a san ko su waye ba suka yi.

“A daidai lokacin da mu ke cigaba da binciken ummul’aba’isan faruwar gobarar, mu na gargadin jama’a da su sanya wa bakunansu linzami a yayin da suke furta maganganun dake fitowa daga bakunan nasu, domin kauce wa abubuwan da za su gurgunta zaman lafiya a tsakanin jama’ar Jihar Kogi da kuma sauran kabilu dake  jihar.

“Jihar Kogi na farin cikin yadda kabilu daban-daban, irinsu Fulani da Bassa da Nupawa da sauransu ke zaune lafiya da junansu, kuma suke harkokinsu ba tare da wata matsala ba a cikin jihar.

“Tuni aka umarci Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha ta jihar da shugaban karamar hukumar Kabba Bunu da kuma Mai Bai Wa Gwamna Shawara Akan Sha’anin Tsaro da su gaggauta gano dalilin  afkuwar gobarar tare da zakulo wadanda suke da hannu a lamarin komai matsayinsu ko kabilarsu, domin ganin sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu.

“Mu na jajenta wa al’ummar Iluke da dukkan wadanda lamarin ya shafa. Mai Girma Gwamnan jihar ta Kogi cikin gaggawa ya bada umarnin gyara makarantar, domin tabbatar da ganin dalibai sun cigaba da karatunsu,” inji sanarwar.

A bangare guda kuwa, kungiyar kare muradin Fulani makiyaya ta kasa (MACBAN) reshen Jihar Kogi, ta gode wa Gwamna Bello a bisa matakan da ya dauka game da zargin da aka yi wa makiyayan.

Kungiyar ta ce, gwamnan ya gudanar da kwakkwaran bincike kuma ya gano cewa ba Fulani makiyaya ba ne suka banka wa makarantar wuta.

“Muna jaddada godiyarmu ga gwamna da kuma mai ba shi shawara akan sha’anin tsaro a bisa gudanar da bincike na hakika,” inji kungiyar a sanarwar da Sakataren MACBAN reshen jihar, Malam Adamu Abubakar, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana godiyarsa a madadin kungiyar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji yada labaran kanzon kurege da ka iya gurgunta zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma. Ya ce, bai ga dalilin da zai sa haka siddan makiyaya su banka wa makaranta wuta ba.

“Muna zaman lafiya a nan Jihar Kogi, ba kamar wasu jihohi ba. Don Allah kada wani ya zo ya haddasa fitina a tsakaninmu,” inji Abubakar.

Daga nan sai ya yi addu’ar Allah ya bai wa Gwamna Yahaya Bello basira, hikima, lafiya da kuma kwarin gwiwar kammala ayyukan da ya faro a jihar.

Exit mobile version