Gobarar Sakkwato: Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Tambuwal

Hutun Kirsimeti

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Kakkarfar tawagar Gwamnatin Tarayya ta jajantawa Gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato a yau Litinin kan ibtila’in gobarar kasuwar Sakkwato da ta kone a ranar Talatar makon jiya.

Wakilan na Gwamnatin Tarayya sun taho ne a karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko, Ministan Sadarwa Ali Isa Pantami, Ministar Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar Faruk da Ministan Lamurran ‘Yan Sanda, Maigari Dingyadi.

A jawabinsa, Gambari ya bayyyana gobarar a matsayin abin jimami maras misaltuwa wanda ya girgiza Shugaba Muhammadu Buhari matuka a gobarar wadda ba wai kawai za ta shafi ‘yan kasuwa ba, ta kuma taba tattalin arzikin Jiha.

“Shugaban Kasa ya umurce mu da mu zo domin mu jajantawa al’ummar wannan Jiha a madadin Gwamnatin Tarayya kuma a tabbatar maku cewar Gwamnatinsa za ta taimaka domin sake gina kasuwar.”

A jawabinsa, Sanata Aliyu Wamakko wanda ke wakiltar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya bayyyana kaduwa da jimamin afkuwar gobarar wadda ya ce ta kidima Shugaban Kasa wanda ya so ya zo da kansa amma saboda yanayin aiki ya turo tawaga mai karfi.

Da yake jawabi, Gwamna Tambuwal ya godewa Shugaba Muhammadu Buhari kan nuna kulawar gaske tare da turo kakkarfar tawagar domin jajanta masu a lokacin na kalubale.    Ya ce kasuwar ba wai kawai al’ummar Sakkwato ke amfana da ita ba, har da al’ummar kasashen waje.

Ya ce Gwamnatin Jiha za ta himmatu domin sake gina kasuwar da kuma tallafawa ‘yan kasuwar.

Gwamnan ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sa hannun domin ganin an sake gina kasuwar tare da tallafawa ‘yan kasuwar. Ya ce kasuwar na da shaguna 14, 000, daga baya aka yi karin 2, 000 na wucin gadi wadanda ya ce bakidaya ta na da shaguna 16, 000. Ya ce kashi 60 na kasuwar ya kone bakidaya.

Exit mobile version