Balarabe Abdullahi" />

Gobe FRSC Za Ta Fara Binciken Lasisin Ababen Hawa A Zariya

Lasisin

A gobe Laraba hukumar kiyaye Hadurra ta kasa da ke kula da shiyyar Zariya, wadda ofishinta ke Zariya, za ta fara binciken ma su Keke Napep, da ba su da lasisi, amma su na amfani da abubuwan hawansu, ba tare da mallakar lasisi ba.

Babbar jami’ar hukumar da ke kula da ke kula da bayar da lasisin a Zariya, Madam Esther Markus Labule ta bayyana haka, a lokacin da ta jagoranci taro da wadanda ke amfani da Keke Napep a shiyyar Zariya.

Aikin bayare da Lasisin da za a fara a ranar Larabar da ta gabata, a cewar Madam Markus Labule, aikin hadin gwiwa ne da hukumar tattara kudin shiga ta jihar Kaduna, ban a hukumar ce ita kadai ba.

Ta kara da cewar, tun daga babban ofishin wannan hukuma daga Abuja, su ka bayar da umurnin lallai a fara wannan aiki a gobe laraba, inda a ke sa ran kwashe wasu lokuta dama dama a na yi a sassan Zariya da kuma shiyya ta daya baki daya.

A kan haka ne Madam Esther Labule ta yi kira ga ma su amfani da keken Napep da suke yin haya da su tabbatar sun je ofishin hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kaduna da ke Zariya domin karban sabon lasisin da zai ba su damar ci gaba da amfani da keke Napep da suka mallaka, kamar yadda dokokin tuki ya tanada ga duk wan da zai hau titi.

Alhaji Yahaya Idris, shi ne babban jami’in da ke hulda da manema labarai a wannan hukuma da ke shiyya ta daya, ya na cikin wadanda su ka yi jawabi a wajen taron, da ya gudana a jiya Littinin a harabar hukumar da ke Zariya.

Alhaji Yahaya Idris, wanda kuma shi ne majidadin Sarkin Zurun Zazzau, ya yi kira ga daukacin wadanda suka halarci taron, kasancewarsu wakilan sauran wadanda ke amfani da ma su amfani da Keke Napep, da lallai su zauna da sauran mambobinsu, su yi bayanin abubuwanda a ka tattauna a wajen taron, domin su san abin da zai gudana a gobe laraba.

Majidadin Sarkin Zurun Zazzau, Alhaji Yahaya Idris, ya kuma tabbatar wa masu amfani da Keke Napep, hukumar kiyaye hadurra da ke kula da shiyyar Zariya, za ta ci gaba da hada hannu da ma su abubuwan hawa da su ke wannan shiyya, domin tabbatar da ko wace doka da gwamnati ta gindaya ga ma su abubuwan hawa da suke wannan shiyya mai ofishi a Zariya.

A gefe guda, shugabanni da wakilan ma su amfani da Keke Napep da su ka fito daga kananan hukumomin Sabon gari da kuma Zariya, Alhaji Mohammed Abubakar Garba shugaban kungiyar ma su haya da Keke Napep a karamar hukumar Sabon gari da Alhaki Adamu Abubakar, shugaba a Kofar Doka da kuma Alhaji Umar Shehu daga karamar hukumar Sabon gari, dukkansu, sun nuna matukar jin dadinsu ga hukumar kiyaye hadurra ta kasa da a duk lokaci, su kan kira su zuwa ofishinsu, domin tattauna wasu abubuwa da su ka shafi yadda za su yi amfani da hanyoyi da kuma in wata doka ta zo gare su, sai suka yi kira garesu da su ci gaba da yadda suke yi, domin samun mafita da ma su abubuwan hawa ke fuskanta a shiyyar Zariya’.

Wadanda aka ambata, sun lashi takobin ba wannan hukuma ta kiyaye hadurra duk goyon bayan da suke bukata, a duk lokacin da bukatar haka ta motsa a nan gaba.

Exit mobile version