Bisa dogaro da rahotanni da aka samu na ganin jinjirin watan Ramadan a wasu garuruwa, Masarautar Sokoto ta bayyana gobe Alhamis 17 Ga watan Mayu a matsayin ranar da za a fara azumin watan Ramadan.
Ramadan shine watan da yafi kowanne alfarma a cikin jiran watanni goma sha biyu na Musulunci.
Dafatan Allah ya karbe ibadun mu gaba daya.