Muhammad A. Abubakar" />

Gobe Za A Karrama Dr. Dauda Lawal Da Lambar Yabo

A gobe ne wata kungiya mai suna ‘Rebuild Zamfara Initiative’ za ta karrama Dr. Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau) da lambar yabo.

Wannan dai karramawa an shiryata ne dn ganin irin ayyukan taimakon al’umma da raya kasa da Gamjin Gusau din yake ta faman gudanarwa a Jihar Zamfara.

Idan dai ba a manta ba, a makonni biyu da suka gabata ne gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kaddamar da jerin wasu ayyuka da Dr. Dauda ya yi a wasu sassan Jihar. Inda a wurin Gwamnan ya yabawa Dr. Dauda, ya kuma yi fatan sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da shi wurin ayyukan alheri.

 

Exit mobile version