Gobe Za A Yi Jana’izar Mai Shari’a Idris Kutigi

A yau Talata iyalan tsohon alkalin-alkalan Nijeriya, mai shara’a Idris Kutugi, da Allah ya yi ma Rasuwa, suka sanar da shirye-shiryen jana’izar shi, za a kawo gawar mai shari’ar ne daga birnin Landan, inda ya rasun, a koma gobe za a mishi jana’iza yadda addinin Musulunci ya tanada.

Za a yi jana’izar ne karfe 2:00 na rana a babban masallacin kasa, daga nan za a birni shi a makabartar Gudu, sannan za ayi addu’ar uku a ranar Alhamis a gidan marigayin da ke Asokoro, Abuja, za a yi addu’ar ukun a fadar Etsu Nupe dake Bida, da kuma mahaifar marigayin wato garin Kutigi, jihar Neja.

Mai shari’ar ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan dake kasar Ingila, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya rike mukamin kwamishinan shari’a na jihar Neja, ya fara aiki da kotun koli na Nijeriya a shekarar 1992, ya rike matsayin babban alkalin Nijeriya daga shekarar 2007 zuwa 2009.

Exit mobile version