Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta tsayar da ranar Alhamis domin fara sayar da tikitin kallon wasannin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Kafar sadarwa BBC Hausa ta nakalto cewar tuni hukumar FIFA ta ce masu sha’awar kallon gasar za su iya neman tikitin a shafinta na Intanet wanda ta shirya sayar wa mataki biyu.
Za kuma ta sayar da shi ne mafi Karancin kudi fam 79 a wasannin zagaye na biyu zuwa fam 829 kuDin wasan Karshe da za a yi a Moscow.
FIFA za ta fara sayar da tikiti a matakin farko tsakanin 16 zuwa 28 ga watan Nuwamba, sannan ta sayar a karo na biyu tsakanin 18 ga watan Afirilu zuwa 15 ga watan Yulin 2018.
Za a fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yuni, inda Rasha mai masukin baKi za ta buga wasanta a filin Luzhniki da ke Moscow.