Connect with us

SIYASA

Gombe 2019: Waye Zai Maye Gurbin Gwamna Dankwambo?

Published

on

A 2019 ne ake sa ran Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo zai kammala wa’adinsa karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Gombe, domin an sake zabansa a matsayin gwamnan jihar Gombe a babban zaben 2015 a karkashin jam’iyyar PDP.

Tunin jam’iyyu suka ja damarar maye gurbin gwamnan da zai karasa wa’adinsa kwanan nan, inda jam’iyyar da ke mulki a jihar ta PDP ta ja damararta na sake fitar da sabon gwamna, a yayin da jam’iyyun adawa irin su (APC) suka fara nuna sha’awarsu na sauya gwamnan jihar Gombe a babban zaben 2019 da ke harararmu kwanan nan.

 

 

 

A bisa haka ne wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ya tsunduma cikin jihar ta Gombe domin nazarta ‘yan takarar da suka fito suke neman wannan kujerar ta gwamna a jam’iyyar PDP da kuma jam’iyyar adawa ta APC. alamu dai na nuni da cewar za a sake jan damarar fafata neman wannan kujerar a tsakanin APC da PDP wanda fitattun ‘yan takara suka fito a cikin jam’iyyun, kamar yadda wakilinmu zai zayyano jerinsu.

‘Yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP:

Bala Bello Tinka, Jamilu Isiaku Gwmna, Hassan Muhammad, Dakta Mohammed Isa Wade, Abubakar Walama, Inuwa (Janjasco), Bayero Nafada, Umar Bello, da kuma Haruna Garba, wadannan sune suke neman kujerar gwamnan a karkashin jam’iyya mai mulki a jihar ta PDP.

Masu neman kujerar gwamna a karkashin APC sun hada da:

Abubakar Habu Muazu, Farouk Bamusa, Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, Inuwa Yahaya, Jibrin Danbarde, Umaru Kwairanga, Abdullahi Idris Umar, da kuma Ahmed Khamisu Mailantarki, dukkanin wadannan suna neman jam’iyyar APC ta basu zarafin neman kujerar, wanda in suka samu za su gigita jam’iyya mai mulki ganin cewar ‘yan APC sun dage sai sun kwaci mulki a hanun PDP.

’Yan takarar APC da ake hasashen za su kai labari; sun hada da Alhaji Musa Umar Farook wanda ya fi shahara da suna Farouk Bamusa, daya ne daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar APC kana wani kasurgumin dan kasuwa ne, gogaggen dan siyasa wanda ya takara matakai daban-daban a siyasar kasar nan.

Alhaji Farook Bamusa ya fito ne daga karamar hukumar Kwami, yana da sarautar gargaji ya ta ‘Sarkin Arewa Gombe’. Kawo yanzu a sakamakon hasashen zai iya kaiwa ga nasara ya fuskaci muhimman kalubale kan wannan kujerar da yake nema musamman daga wasu ‘yan takarar gwamnan da kuma wasu mukarraban gwamnan Gombe.

UMAR FAROOK Bamusa an haifesa ne dai a ranar 13 ga watan Maris 1963 a jihar ta Gombe, ya yi aure har Allah ya bashi sarautar Sarkin Arewan Gombe a sakamakon gogewarsa kan harkar kasuwanci da siyasa hadi da taimakon jama’an jihar. Ya halarci jami’ar Maiduguri a tsakinin watan Satumbar 1981 zuwa Yuli 1985 ya samu shaidar digirin farko ne a fannin gudanar da kasuwanci (Business Management), ya kuma yi sakandarin gwamnati da ke Gombe a 1980, a yayin da kuma kundun tarihinsa ya nuna ya yi karatun Firamare ne a Jankai da ke Gombe a tsakanin 1968 – 1975.

A bangaren kwarewarsa kan aiki kuwa, Farouk ya taba kasancewa mataimakin Daraktan gudanarwa na kamfanin ‘Image Technologies Limited’ a shekarar 1989 ne aka bashi aiki a matsayin babban jami’in sayar da kayyaki na kamganin Honeywell Computers Limited, ya yi aikin bautar kasarsa ne a tsohowar jihar Imo a 1985 zuwa 1986.

Wasu aiyukan da ya yi sun hada da mamba a majalisar zastarwa na jami’ar Jos daga 2007 – 2012; mamba a Bision 2020; mamba a kwamitin yakin neman zaben Muhammad Buhari Campaing Organisation, da dai sauransu.

Alhaji Farouk ya yi aiki a wasu ma’aikatu daban-daban wanda har ya kai muhimmman matakai, a bisa jajircewarsa da kwazonsa ya samu lambobin yabo masu tulin yawa wanda har ta kai shi ga samun lambobin karramawa.

Kawo yanzu ya kasance wanda ya kaddamar da shirin tallafi ga jama’a masu tarin yawa, a wani lokaci ya raba kayyakin sallah wanda jama’a da dama suka ci gajiyarsa, a baya-bayan nan ma ya yi irin wannan aikin wanda jama’an musulmai da dama sun yaba masa kan wannan sa’ayin. A bisa haka yana da damar zama gwamnan jihar Gombe muddin APC ta bashi zarafi.

 

ABUBAKAR HABU MU’AZU

Alhaji Abubakar Habu Mu’azu shi ma yana tsumawayar tikitin tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC.

 

Habu Muazu wanda ke neman kujerar gwamna a jam’iyyar APC, ya taba fadi kan cewar bai kamata jama’an jihar su ci gaba da barin PDP tana ci gaba da jan ragamar jihar a cewarsa APC ta fi cancantar shugabantar jihar domin shimfida muhimman aiyukan raya jihar.

 

AHMED KHAMISU MAILANTARKI

Ahmed Khamisu Mailantarki wanda shi ma yake neman gwamna a jam’iyyar APC, ya shaida cewar yana neman kujerar gwamnan ne domin gwamna Ibrahim Hassan Dangwanbo ya gaza wajen gina jihar, inda ya shaida cewar yana da muradin kyautata rayuwar jama’an jihar.

 

Ya bukaci jam’iyyar APC ta tsaida shi neman gwamnan jihar, a cewarsa jam’iyyar tana bukatar wani nagartacce kuma tsohon dan siyasa wanda zai iya kwace mulki daga hanun PDP a jihar.

 

IBRAHIM DASUKI JALO WAZIRI

Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, ya kasance masani kan harkokin gudanar da mulki, domin ya taba kasance shugaban karamar hukumar Gombe a lokacin zamanin gwamna Muhammed Danjuma Goje, shi ne ya kasance shugaban kungiyar shugabanin kananan hukumomi ALGON a wancan lokacin, ya fito neman kujerar gwamnan a karkashin APC tare da sauran masu neman wannan kujerar. Don haka na da damar zama gwamna idan ya samu tikiti a APC.

 

BARISTA ABDULLAHI IDRIS UMAR

Yana cikin masu neman APC ta basu tikitin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe, gogaggen dan siyasa ne wanda muddin aka bashi zarafi zai kyautata jihar kamar yadda ya bayyana da kansa, ya taba kasancewa dan majalisa mai wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya, ya kuma taba zama Mininsta a gwamnan Yar’adua/Jonathan.

 

MOHAMMED INUWA YAHAYA

Mohammed Inuwu Yahaya, shi ma dai yana neman APC ta tsaida shi domin neman wannan kujerar, ya zage damtse wajen neman wannan kujerar, a wata hira da jaridar Leadership Ayau ta taba yi da shi kan neman kujerar gwamnan Gombe da yake yi, ya bayyana cewar ya fito ne domin kawo wa jihar Gombe gyara ta fuskacin da gwamnati mai cit a lalata, ya sha alwashin tabbatar da gyara barnar da aka rigaya aka yi.

Inuwa Yahaya ya yi takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2015 inda gwamna Ibrahim Hassan DanKwambo na PDP ya kada shi, a bisa fito na fito da yayi a wancan zaben na 2015 yana da damar zama gwamnan jihar Gombe muddin APC ta tsaida shi.

A wani hirarsa da Leadershi kan neman kujerarsa ta gwamna ya ce, “Abun da zan ce ga masoya da magoya baya na, shi ne Muhammad Inuwa Yahaya yana nan kuma da yardar Allah ina cikin takara, kuma zan tsaya takara, kuma cikin yardar Allah zai kai ga nasara a wannan karon, domin an sha mu mun warke mun san hanyar da za mu bi, kuma in Allah ya yarda za mu yi mulki a jihar Gombe, masoyanmu su san da wannan ina shirye kuma na fito neman gwamna a 2019 a jihata ta Gombe,”

“Mu ai ba ma wa mu ba, wa magoya bayanmu ma sun hadu sun hade kansu sun yi zama kashi-kashi kuma har yanzu ana kan wannan zaman, APC a dinke take a Gombe, domin daman Baba Buhari ya fada mana cewar jiki magayi, to jikinmu ya gaya mana, yanzu mun hadu mun hade kuma za mu kai ga samun nasara cikin yarda Allah a tsakaninmu”.

Inuwa dai na da damar zama gwamna a bisa kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka fafata da gwamna mai ci a 2015.

Kawo yanzu dai ido ya koma kan jam’iyyar APC a jihar wajen ganin shin za ta iya kwace mulki a jihar Gombe ko yaya?

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: