Gwamnatin Jihar Gombe ta bada kwangila ta fiye da Naira biliyan 2 da miliyan 900 don aikin dinke kwarin Jami’a Mallakar Jihar Gombe GSU zuwa Malam Inna ga kamfanin Triacta Nigeria Limited ta hannun shirin magance zaizayar kasa da alkinta ruwa na NEWMAP.
Da ya ke jawabi yayin sanya hanu kan yarjejeniyar a gidan gwamnati, Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya ce sanya hanu kan kwangilar wata shaida ce ta himmatuwar gwamnatinsa na magance matsalolin da kwarurruka ke haifarwa a jihar.
Ya ce gwamnatin ta damu da aukuwar ambaliya akai-akai a jihar sanadiyyar kwarurrukan dake jihar, wadanda ke lalata ayyukan raya kasa da janyo asarar rayuka da dukiyoyi dama sana’o’i da harkokin kasuwancin jama’a.
Gwamnan ya ce sanya hanu kan yarjejeniyar, wani jajircewan hadin gwiwa ne don kyautata muhalli da kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar yin hadin gwiwa da bankin duniya da sauran hukumomin ci gaba, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da ingantuwar mummunan halin da muhalli ya shiga tare da magance matsalolin kwarurruka a jihar.
Sai ya kira yi shirin magance zaizayar kasa da alkinta ruwa na NEWMAP din reshen Jihar Gombe da ma’aikatar muhalli da gandun daji ta jihar su tabbatar cewa kamfanin ya kammala aikin a kan lokacin da aka kayyade kuma su tabbatar da bin ka’idojin inganci da nagarta a aikin.
Da take jawabi tun farko, Kwamishinar muhalli da gandun daji ta jihar Dr. Hussaina Danjuma Goje, ta ce an bada kwangilar ce bisa ka’idar Bankin Duniya da sharudan kamfanin Triacta Nigeria Limited biyo bayan karbar shawarwarin tawagar sanya ido ta Bankin Duniya.
A nashi tsokacin bayan sanya hanu kan kwangilar, Engr. Imran Amin Khan wadda ya tsaya a madadin kamfanin na Triacta Nigeria Limited, ya ce kamfaninsu yana da dogon tarihin gudanar da ayyukan raya kasa tsakaninsa da Jihar Gombe, yana mai bada tabbacin gudanar da aiki mai nagarta cikin wa’adin da aka debarwa aikin.
Kamar yadda Ismala Uba Misilli, Hadimin gwamnan Gombe ke nakaltowa, jami’in kula da ayyukan hukumar ta NEWMAP a Jihar Gombe Injiniya Mohammed Garba da jami’in kula da kwangiloli na jiha Abdulkadir Ibrahim Jalo ne suka sanya hanu kan kwangilar a madadin gwamnatin Jihar Gombe, yayin da Imran Amin Khan da Lateef Abboud suka sanya hanu a madadin kamfanin na Triacta Nigeria Limited.
Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar...