Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi hasashen cewa ya zuwa shekara ta 2030, Jihar za ta kasance dandamalin ci gaba, zaman lafiya da samar da dimbin damarmakin bunkasar arziki ga al’ummar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan tsarin ci gaba na jihar Gombe na tsawon shekaru 10, yana mai cewa jihar tana da duk abinda ake bukata na cimma buruka da muradunta.
Ya ce, “Muna da dimbin jama’a masu hazaka da basirar tafiyar da masana’antu, da dimbin albarkatun kasa, da garuruwa masu bunkasa cikin sauri, da zaman lafiya da arzikin noma da ruwa wadanda za su zaburar da burin mu na zama zakaran gwajin dafi a kasar nan.”
Ya ce tsarin ci gaban na shekaru 10, ya dace da muradun ci gaba mai daurewa na Majalisar Dinkin Duniya, da binciken tantance bukatun al’ummar da gwamnatinsa ta gudanar daga hawanta kan karaga.
Gwamnan ya ce hadin kan ‘ya’yan jihar maza da mata yana nuni da himmatuwa da nuna azamar su na ganin ci gaban jihar.
Ya ce kasancewar jihar a tsakiyar arewa maso gabas, ya maishe ta cibiyar bunkasar kasuwanci, tattalin arziki da zamantakewa, yana mai cewa karon farko a tarihin jihar, gwamnatinsa na shirin samar da kundin da zai tabbatar da ayyuka da shirye-shirye masu nagarta don amfanin al’ummar jihar.
Gwamna Inuwa sai ya yabawa kwamitin gudanar da tsare-tsaren wannan jadawalin ci gaba na shekaru 10, bisa kokarinsa na shirya tattaunawar masu ruwa da tsaki daga matakan gundumomi zuwa kananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma yabawa asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da asusun tallafawa kidayar jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) bisa gagarumar rawar da suka taka wajen tafiyar da ayyukan kwamitocin tsarawa da gudanar da wannan aiki.
Ya kuma yabawa fitattun ‘ya’yan jihar maza da mata da suka bada gudunmowa a zahirance ko ta hanyar na’urorin ganin juna daga nesa, yana mai bayyana su a matsayin ‘yan kishin kasa wadanda gudunmawarsu za ta taimaka gaya wajen tsara jadawalin ci gaban.
Shugaban kwamitin gudanarwar tsara jadawalin ci gaban na shekaru 10, kuma mataimakin gwamnan jihar, Dr Manasseh Daniel Jatau, ya ce gwamnan ya nuna kishi da aniya mai girma don samar da ci gaba a lungu da sako na jihar.
Ya ce sauye-sauyen da ake samu a sashin ilimi da lafiya da samar da ayyuka, da rage zaman banza da kafa cibiyar masana’antu dama karfafa harkar noma a jihar, wasu ‘yan manuniya ne dake tabbatar da cewa gwamnan da gaske yake wajen kara farfado da jihar ta cikin wannan tsarin ci gaba da ya kirkiro.
Babban jagoran tawagar kwararru masu tsara wannan jadawalin ci gaba Farfesa Emmanuel Onwioduokit, wanda ya gabatar da jawabi kan abubuwan da jadawalin ci gaban ya kunsa, ya ce an shirya tsarin ne don samar wa jihar ci gaba mai dogon zango.
A jawabinta na fatan alkairi ga taron ta kafar na’urar ganin juna daga nesa, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta yabawa Gwamna Inuwa Yahaya dama kwamitin bisa samar da wanna tsarin ci gaba da tace zai taimaka gaya wajen saukaka harkokin ci gaba a jihar.
Ta ce Majalisar ta Dinkin Duniya za ta yi aiki kafada da kafada da Gwamnatin Jihar Gombe don tabbatar da aiwatar tsarin ci gaban da zai amfani al’ummar jihar.
Sauran hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da suka nuna goyon bayan su ga Jihar ta Gombe kan wannan tsarin sun hada da asusun tallafawa yara UNICEF da shirin samar da ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya UNDP da asusun tallafawa kidaya UNFPA da ofishin muradun ci gaba mai daurewa SDGs da kungiyoyin fararen fula a jihar ta Gombe.
Haka nan tsohon gwamnan jihar ta Gombe na farko a mulkin soja Group Captain T. I. Orji mai murabus ya gabatar da jawabin fatan alkairi.
Fitattun yayan jihar maza da mata da suka hada da tsohon ministan babban birnin tarayya Dr. Aliyu Modibbo Umar da tsohon karamin ministan makamashi Malam Murtala Aliyu da na muhalli Surbeyor Sulaiman Hassan Jara, da babban daraktan hukumar kare muhalli ta kasa NESREA Farfesa Aliyu Jauro da tsohon babban Daraktan hukumar PENCOM, Malam M.K Ahmad, da Sarkin Fulanin Gombe, Alhaji Umaru Kwairanga da wasu da dama sun gabatar da jawabin gudunmawa kan yadda za a cimma nasarar aiwatar da tsarin don moriyar al’ummar jihar.