Khalid Idris Doya" />

Gombe Za Ta Gina Burtsatsai 661 

A kokarinta na bunkasawa da kyautata sashin samar da ruwa mai tsafta ga al’umma, gwamnatin jihar Gombe za ta gina fanfunan tuka-tuka ciki har da masu amfani da hasken rana guda dari shida da sittin da daya (661) da za a kafasu a sassan kananan hukumomi 11 da su ke jihar.

Janar Manaja na hukumar samar da ruwa da tsaftar muhalli a yankunan karkara (RUWASA) Alhaji Abdurrakib Muhammad shine ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Gombe ranar Talata.

Janar Manajan ya kuma shaida cewar daukan matakin na zuwa ne a sakamakon tsananin bukatar hakan da al’umman yankunan ke yi, inda ya ce sun gano jama’a na bukatar hakan daga nan suka dauki matakin samar musu da fanfunan.

Ya shaida cewar gwamnatin ta samu rancen kudi daga bankin raya Afurka (ADB) don haka ma dukkanin tsare-tsaren fara aikin sun kankama da ya ke shan alwashin cewar za su fara aiwatar da aikin nan ba da jimawa ba.

“Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kudurinsa na samar da ruwa mai tsafta a tsakanin jama’a domin gayar muhimmancin da ruwa ke da shi a sha’anin rayuwar jama’a. Da irin wanna himmar muka tashi tsaye domin kyautata sashin ruwan sha da na amfanin yau da kullum.”

Muhammad ya kuma kara da cewa baya ga bohul-bohul da za su samar, za kuma a gina wasu abubuwan more rayuwar al’umma da suka hada da Bayan gida (Masai), makarantu, cibiyoyin lafiya da sauransu a sassa daban-daban.

A cewarshi gina sabbin Masai na zamani zai taimaka wajen rage yawaitar kashi barkatai da jama’a ke yi wanda hakan na jawo illa ga lafiyarsu, yana mai bayanin cewar sabbin Masai da za a gina za su taimaka matuka wa jama’a musamman talakawa.

Ya kuma kara da cewa yin bahaya a waje na da matukar illa ga lafiyar da tabarbara kiwon lafiya hadi da shafan tattalin arzikin jihar.

Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su dauki shawarorin da ake basu na kiyaye tsaftar muhalli da ta jiki domin kwalliya take biyan kudin sabulu na inganta kiwon lafiya.

Ya nanata cewar gwamnatin jihar ta dukufa ta fuskacin samar da ruwa mai tsafta ga jama’a, don haka ne ya nemi su ma jama’ar da su bada tasu gudunmawar.

Exit mobile version