Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Goran Duma: Kallon Me Ake Wa ‘Ya’ya Mata?

by Tayo Adelaja
September 20, 2017
in NAZARI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Rayuwar Duniya cike ta ke da kalubale, duk da fadi tashi da kiraye-kirayen da ake ta yi kan ilimantar da ‘ya’ya mata da ba su damar samun ingantaccen ilimi musamman na Firamare da karama da babbar Sakandire, amma duk da haka wasu na fuskantar tarnakin rayuwa da samun cikas ga cikar wannan kuduri da aka cimmawa.

Daga Bishir Suleiman

samndaads

Bincike ya bayyana har yanzu kashi talatin da uku 33 na mata ke samun shiga Makarantun boko a Nijeriya, kuma mafi yawancinsu ba su samun damar kammala ko karamar sakandire, ake cire su a yi masu aure, sakamakon girma jiki da kuma samun mazajen auren da wasun su ke yi da wuri, da sauran dalilai na Mahaifan ‘ya’ya.

Daga cikin kalubalan da mata ke fuskanta a kwai na al’adu wadda ita ce take masu tarnaki ga barin su samu ilmin zamani da ake son kowace diya mace ta samu, wadda a ganin wasu mahaifan na ganin bai da wata fa’ida a ilmantar da mace, domin in ta samu ilimi ba za ta yi biyayyar aure ba. Kuma ma tana iya rasa manema, har ta kai ta zama abin da Hausawa ke kira da Sabagiji. Al’adu su na ganin macen da samu ilimin boko ana ma ta kallon na musamman a cikin al’ummar da take rayuwa a cikinta, na zargi da aibanta da nuna wa samari isa da jin kai, Musamman a cikin wasu kauyikan.

Duk da wannan kallon da al’adu da zamantakewa ke wa ilimin boko, amma bai fidda a’i a ga rogo ba, ga kalubalen rayuwar ‘ya’ya mata ba, domin har yanzu akwai abin na nan, dan za a cire yarinya daga makaranta in ta samu miji an mata aure nan ma wani sabon ilimin ne, domin wasu kan fada hannun mazaje masu tafiya ci rani a wasu jihohi, wadda in sun dawo karkarar su tamkar wasuAlhadawa, da haka za su burge tsaffin kauyukan nasu, musamman mata har su kwadaitu da san ba su ‘ya’yan su aure, kuma da zarar an yi auren wasu in sun sa gaba ba su kara waiwayo baya, sai su share wata biyar zuwa bakwai ba su leko gida ba. Iyakar su da iyalan  duk bayan sati biyu su turo masu  katin 1500, wadda in su toro masu, matan su sayar 1200, da ita za su yi bukatocin tayuwa ta yau da kullum da ta hada da sayen abinci, ruwa, man shafawa da yar hoda. Ba batun sutura ake ba, domin ‘yar wadda aka yi a lokacin biki sai a shafe haihuwa uku ba a kara ba, ba a batun noma, domin dama kudi ake turowa, yanzu kuwa an yi iyali kudin da ake turowa ta katin waya sun hana turo kudin noma. Akwai ma wanda ba su da damar turo katin wayar, sai dai in wasu za su taho gida su aiko wasu ma kan share fiye sa shekara biyu, sannan a aiko. Wasu  matan tun da suka yi aure basu taba wata cif da mazajen su ba a gida. Saboda irin dogon zangon da mazajen kan yi wajen nema, shi ke haifar da kowamar matan gidajen iyayen su.  Wato abin nan, da Bahushe ke kyama kan tabbata, na ka sayar da Akuya ta dawo tana ci ma danga, sai mace ta share dogon lokaci a gidan su, sai idan mijin ya zo ta ke komawa dakin ta.

A wani kalubale kuwa sai in mace ta samu juna biyu, bai cimaka ba zuwa duba lafiyar uwa da abin da ke jikinta, haka za a yi ta laulayi har lokacin da Allah zai fitar da abin da zai fitar da abin da ke ciki, wadda ta samu ta sauka lafiya tai barka, sai kuma na kalubalen fafutukar abin da za ta dan hada a uwar hanjinta ta samu ruwan mamar da za ta shayar da abin da ta haifa, domin mafi akasari mazajen ba su nan ake haifuwar,  ba kuma wani tanadi suke mata ba, sai dai uwar diyar tai ta kai koma wajen ciyar da ‘yarta, dangin miji kuwa sun kokarta su leko barka, da dan tarfin gero a tafarfara, domin su riga sun raba jiha tun lokacin da ya bar bada kudin noma, haka kowace ‘yar barka za ta dan leko ta kama gabanta don ba cimaka. Har dai a samu a yi suna.

Raino wani kalubale ne, domin babu cima balle abin da aka haifa, ya samu kwari da ingantaciyar lafiya, ba kuma ta zuwa asibiti ake ba, da cikin ma ba a je awo ba, balle ya zo duniya.

A na cikin haka batun karin aure ya ke tasowa, da zaran mazaje sun ga an yi masu haihuwa kuma abokanan su mazauna gida na ta kara aure sai suma su shiga fagen kara aure, kwatsam sai kara jefo ma shi wata mai tsautsan, ita ma da an samu sati biyar da amarci zuwa shidda ya bar su ya kama gabansa. Ita ma ta bi layin gadon matsalolin da duk waccan ke fuskanta da ga mijin, sai dai kuma gara ita a bangaren iyayen mijin domin ita ta farin za ta shiga tasku da kara kwomadewa kamar dan giginya, musamman in daukin angonci ya sa mijin ya dan leko gida bayan tafiyar sa da wata biyu ko uku.

SendShareTweetShare
Previous Post

MUKALAR LARABA: Ganin Dala Ba Shiga Birni Ba: Yunkurin Rage Shekarun Yin Takara A Nijeriya

Next Post

Kasashe 10 Da Suka Fi Hadari A Afirka

RelatedPosts

Mazan Jiya

Tunawa Da Yan Mazan Jiya: Yaushe Zai Tashi Daga Biki Zuwa Aiki? 24

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

An kirkiro da ranar tuna wa da sojoji yan mazan...

Arewa

An Yi Wa Arewa  Nisa A Kasar Nan

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Har yanzu duniyar  Arewacin Nijeriya ba mu dauka duniyar kudu...

Bayanan Sirri

Rashin Tsaro: Shugaba Buhari, Monguno Da Aikin Tattara Bayanan Sirri

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Tsaro shi ne abu na farko kuma...

Next Post

Kasashe 10 Da Suka Fi Hadari A Afirka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version