GORON JUMA’A

Juma'a

Sako Daga Abubakar Tijjani:

Assalamu alaikum al’umar Musulmi baki daya, ina yi wa kowa da kowa fatan alheri, kuma ina yi wa dukkannin Musulmi barka da juma’a, musamman ma abokaina na jami’ar Alhikima da ke Lakwaja , ina gaishe da dan uwana Muhammad Abdullahi da yake Jihar Kano. Ina gaishe da abokina Abdullahi Umar da ke Hadeja, ina gaishe da abokina Nuruddin Muhammad dake Jihar Bauchi.

 

Sako Daga Maryam Umar Ummi:

Assalamu alaikum, ina mika gasuwata ta barka da juma’a  ga al’umma Musulmin duniya baki daya, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina ina yi masa fatan alheri da jinjina gare shi. Ina mika gaisuwata ga jama’ar gidan Alhaji Umar Dan Garba, yayyena da kannena, ina mika gaisuwata ga abokaina wadanda muka yi makarantar Aminu Yusuf da su, ina gaida Habibata, ina gaida Fatima Abdullahi da take Kano, ina gaida Khadija Abdullahi tare da Ummi a Kano, ina mika gaisuwata ga mutanen garimmu Hadeja.

 

Sako Daga Hassan Tijjani Kassim:

 

Assalamu alaikun, ina mika sakon gaisuwa da barka da juma’a zuwa ga daukacin Musulmin duniya baki daya musamman ‘yan uwana ina gaishe da zuri’armu ta Alhaji Tijjani kassim Hadeja, ina gaishe da abokan aikina da ke bankin Keystone, ina yi musu barka da juma’a, ina gaishe da dukkannin abokaina wadanda muka yi Jami’ar Ilori tare.

 

Sako Daga Sani Hassan Korau:

Assalamu alaikum, mika sakona na goron Juma’a ga dukkan daukacin Musulmin duniya baki daya, sannan ina gai da aminina Abdullahi da Sabi’u da Saminu da Ilyasu, da Babangida da Ahmad Garba, da kuma Yahya Musa. Dukkaninsu ian yi musu barka da Juma’a da fatan sun yi Juma’a lafiya. Allah ya sa haka amin.

 

Sako Daga Idris Aliyu Daudawa

Assalamu alaikum jama’a barkanmu da Juma’a. Da farko ina gaida aminina Malam Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki, Rukayyat Idris Aliyu, Suleiman Idris, Muhammad Idris, Fatima Idris, Aisha Idris, Safiyya Idris, Habibu (Kalifa) Idris sai Nana Hauwa’u Idris da fatan kuna nan lafiya.

Exit mobile version