An Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Rashawa

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Kwamishiniyar Shari’ ta Jihar Kebbi, Hajiya Rakiya Haruna Ayuba, ta yabawa Gwamnatin Tarayya kan yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, a cewarsa babu wata gwamnati da za ta samu zaman lafiyar gudanar da aiki matukar akwai bara gurbi a cikinta..

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a Birnin-kebbi, a lokacin da take gabatar da jawabin ga manema labarai na irin nasarorin da ma’aikatar da tke jagoranta ta samu, wanda kungiyar ‘ya jarida ta jihar kebbi, watau (NUJ) take shirya ga ma’aikatun gwamnatin Jihar Kebbi a kowane wata domin yada manufufin gwamnatin zuwa ga al’umma.

Hajiya Rakiya ta ce, “yakin da cin hanci da rashawa da Gwamnatin tarayya ke yi ya rage almundahana a ofisoshin gwamnati tun daga matakin kananan hukumomi har zuwa jiha, kuma ya taimaka wajen kawo zaman lafiya ga bangaren ilimi na kasar nan, haka zalika ya samar da daidaito a tsakanin al’umma.”

Har ila yau, ta bayyana cewa game da masu laifi dake jiran hukunci su 237 da ke tsare a gidajen yarin Jihar Kebbi daga shekara ta 2015 zuwa 2017, an magance wannan matsalar, musamman don ganin an rage cinkoson mutane a gidajen yarin.

“Gwamnatin da ta shude ta bari gidajen yarin sun cika makil, mutane suna jiran hukunci ko ba a gabatar da su a gaban kotu ba, suna nan kawai ajiye. Wannan sam bai dace ba, yana cikin abubuwan da ofishina ya fara mayar da hankali a kai lokacin da na kama aiki.” In ji ta.

A karshe ta ce, “matsalar masu laifi da ke jiran Shari’a ajiye a gidajen suna da yawa a Nijeriya, wanda Kebbi na cikin wadanda haka ya shafa, amma duk da haka, mun yi iya kokarin mu na rage yawan adadin lamarin zuwa mataki kadan.”

Exit mobile version