Daga Mubakar Umar, Abuja
Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewar tsananin so da kuma goyon bayan da ya rika bawa tsarin mulkin dimukradiyya ne ya sa aka kulle shi a kurkuku tsawon shekaru.
Obasanjo ya fadi haka ne a wata tattaunawar musamman da aka yi da shi a gidan talabijin na CNN, inda ya ce zamansa a gidan kaso babbar nasara ce a rayuwarsa, domin lokacin da ya fito kowa ya ga abinda ya faru.
Haka zalika, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa nasarorin da ya samu cikin shekaru biyu da hayewa kan karagar mulki, inda ya ce akwai bukatar aka kara karfafawa Shugaban gwiwa domin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Da yake magana kan tsarin shugabanci a Afirka, Obasanjo ya ce, lokaci ya yi da ya kamata Shugabannin da Matasa a Afirka su tashi tsaye haikan don magance matsalolin da suka addabi nahiyar, a cewarsa, akwai bukatar matasa su canja daga yadda suke a yanzu.
Obasanjo ya ce, “Tabbas akwai kalubale a gaban al’ummar Afirka, kullum adadin mutane karuwa yake yi, ta yaya za mu yi tunanin ninka abubuwan da muke sarrafawa domin al’ummarmu? Ta yaya za mu samarwa matasa ayyukan yi? Wadannan su ne matsalolin da suka sha gabanmu a halin yanzu, wajibi ne a sauya salon tsarin gudanarwa.
“Bai kamata mu zauna a wuri daya muna shan iska, sannan mu rika tsammanin canji zai zo bagatatan. Lokacin da za mu canja ya yi.” In ji shi.
Da yake tsokaci kan zamansa a gidan yari, Obasanjo ya ce hakan ta faru ne kasancewarsa mutum mai tsananin son tsarin gwamnatin dimukradiyya.
“Maganar da nake yawan yi kan tagomashin tsarin mulkin dimukradiyya shi ne babban dalilin da ya sa aka kulle ni a gidan yari. Cewa da na yi duk sojan da yake son shugabancin kasar nan to ya ajiye kaki, ya tsaya takara a zabe shi, saboda haka suka kulle ni a kurkuku.
“Lokacin da nake tsare, ‘yan Nijeriya sun ga abinda nake fada a zahiri, zaman na da na yi a gidan kaso bai rage ni da komai ba. An ga yadda abubuwa suka canja bayan na fito, inda na zama Shugaban Kasa.
“Ni mutum ne mai tunanin abubuwan alheri, kullum fatana nagari ne. Ina kokarin samar da mafita a duk lokacin da aka shiga matsala.” In ji shi.