Ƙunngiyar masu horar da ‘yan wasa na ƙananun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa dake jihar Bauchi, a tarayyar Najeriya, (Grafca) tayi bikin murnar chika shekaru Goma da kafuwar.
An dai kafa wannan ƙungiyarce a shekara ta 2007, farkon sunan ƙungiyar YOFCA wato (Youth Football Coaches Association Of Bauchi) daga bisani ta Koma GRAFCA, (Grassroot football Coaches Association Of Bauchi,) a shekara 2016.
An ƙirƙiro wannan ƙungiyarce domin tallafawa Ƙananun ƙungiyoyin wasan ƙwallon ƙafa da kuma zaƙulo da ‘yan wasan na cikin gida.
Shuwagabanin ƙungiyar sunyi jerin gwano sanye da riguna mai dauke da tambarin Ƙungiyar ta Grafca, tare da ‘yan wasa yayin nuna farin cikinsu bias irin nasarori da ƙungiyar ta samu da kuma irin gudumawar da suke samu daga gwamnati da kuma hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta (FA) na jihar Bauchi tare da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa.