Abba Ibrahim Wada" />

Greenwood Zai Iya Zama Kamar Ronaldo Ko Messi, Cewar Solkjaer

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa, matashin dan wasan gaba na kungiyar, Marson Greenwood, zai iya zama babban dan wasa kamar Messi ko Ronaldo a nan gaba kadan.

Solkjaer ya bayyana haka ne a hirar da yayi da manema labarai a ya yinda kungiyar ta Manchester United take kokarin fafata wasa da kungiyar Real Soceidad a gasar cinn kofin Europa League wasa na biyu a Ingila
A satin daya gabata ne matashin dan wasan dan asalin kasar Ingila, ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da buga wasa a Manchester United zuwa karshen kakar wasa ta 2025 bayan an dauki lokaci ana tattaunawa.
Cikin kunshin yarjejeniyar dan wasan mai buga gurbin gaba ya amince Manchester United ta kara tsawaita zamansa a Old Trafford kakar wasa daya idan ya cika wa’adinsa kamar yadda kungiyar ta bukata kuma shima ya amince.
A watan Satumba dan wasan mai shekara 19 a duniya ya fara buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasa, kuma yana da kwantiragin da zai kara a kungiyar a watan Yunin shekarar ta 2023 tun farko.
Greenwood ya fara buga wasa a Manchester  United tun daga matasan kungiyar a lokacin yana da shekara bakwai da haihuwa sannan dan wasan ya ci kwallo hudu a karawa 18 a bana, kuma jumulla yana da kwallo 21 a raga a wasanni 82 da ya yi wa Manchester United kawo yanzu.
”Duk wanda yake bibiyar salon buga wasan Greenwood yasan cewa dan wasa ne mai hazaka kuma wanda za’a dade ana gogawa dashi sannan kuma yana taimakawa kungiyarsa a kowanne hali” in ji Solkjaer
Ya ci gaba da cewa “Ina ganin nan gaba kadan idan har ya ci gaba da dagewa zai iya zama kamar Messi ko Ronaldo saboda yana buga wasa tun yana karami irin yadda suma sukayi a lokacin da suna kanana”
Ole Gunnar Solskjaer ya fara sa Greenwood a babbar kungiyar United cikin watan Maris din shekara ta 2019 yana da shekara 17 da kwana 156 a lokacin sannan Greenwood ya fara yi wa Ingila wasa tare da dan kwallon Manchester City, Phil Foden a Nations League da kasar ta doke Iceland 1-0 a watan Satumba.
Sai dai daga baya ‘yan wasan biyu suka bar sansanin, bayan da suka karya dokar hana yada cutar korona amma daga baya kociyan kungiyar, Gareth Southgate ya yafewa ‘yan wasan kuma ya ci gaba da gayyatarsu.
Matashin dan wasa Greenwood dai yana daya daga cikin kwararrun matasan ‘yan wasan da ake ganin tauraruwarsu zata haska a nan gaba duba da irin kokarin da yayi musamman a kakar wasan data gabata wanda ya taimakawa kungiyar ta kammala kakar wasan a matsayi na uku.
Kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana farin cikinsa da samun dan wasa a Manchester United kuma sake sabuwar yarjejeniyar dan wasan kociyan yayi alkawarin ci gaba da taimaka masa domin ganin ya zama shahararren dan wasan kwallo a duniya.

Exit mobile version