Connect with us

WASANNI

Griezman Ya Sake Sabon Kwantaragi Da Atletico Madrid

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta tabbatar da cewa dan wasanta Antonio Greizman ya sake sabon kwantaragi da ita kuma zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa shekara ta 2023 lokacin da kwantaragin nasa zai kare.
Griezman dai yasha suka daga bangaren magoya bayan kungiyar ta Atletico Madrid bayan da sukayi zargin dan wasan yana wasa da tunaninsu inda suka bayyana cewa gwanda ya bayyana cewa zai tafi ko zai zauna su san abinyi.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce dai tayi zawarcin dan wasan a wannan kakar inda a kwanakin baya ma aka bayyana cewa sun amince da yarjejeniyar albashin da zasu dinga bashi idan har ya amince da komawa kungiyar.
A shekarar data gabata ma dai kungiyar Manchester United ta so siyan dan wasan kafin nan ma ya canja shawarar cigaba da zama a kungiyar bayan da aka dakatar da kungiyar daga siyan sababin yan wasa sakamakon kamasu da akayi da laifin siyan yan wasa matasa wadanda basu kai shekara 18 ba a duniya.
Atletico Madrid dai tayi masa alkawarin albashin fam miliyan 17.5 idan ya zauna sannan kuma ta ware fam miliyan 100 domin siyan sababbin yan wasa domin fuskantar kalubale a kakar wasa mai zuwa tare da gogawa da manyan kungiyoyin duniya.
Kungiyar dai ta Atletico a satin daya gabata ta tabbatar da cewa ta kammala yarjejeniya da kungiyar Monaco domin siyan dan wasa Thomas Lemar dan kasar Faransa akan kudi kusan fam miliyan 60 kuma tuni aka saka ranar da za a gwada kafiyar dan wasan.
A yanzu dai dan wasan yana kasar Rasha inda yake wakiltar kasar sa ta Faransa kuma ya zura kwallo a wasan farko da suka buga da kasar Austria da bugun fanareti.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: