CRI Hausa" />

Guangzhou Yana Yin Daidaito Ga Dukkan Bakin Dake Shiga Birnin

Mahukuntan birnin Guangzhou na kasar Sin sun sanar da cewa, suna tafiyar da ayyukansu daidai wa daida ga dukkan baki ’yan kasashen waje dake zaune a birnin tare da bukatarsu dasu kiyaye dokokin cikin gida na yankin game da batun dakile annobar COVID-19.

A taron manema labarai da aka kira a yau Lahadi, daraktan ofishin kula harkokin waje na birnin, Liu Baochun, ya ce, suna tafiyar da ayyukansu na bai daya game da matakan dakile annobar ga dukkan mutanen dake shiga Guangzhou ba tare da yin la’akari da kasashe, ko kabila ko jinsi ba.
Liu ya bayyana cewa, birnin ya inganta matakan gudanar da ayyukansa domin kaucewa samun rashin fatimtar juna ko nuna wata halayyar da bata dace ba sakamakon rashin ingantacciyar hanyar sadarwa da kuma wasu dalilai da suka shafi batun aiwatar da matakan kiwon lafiya.
Cai Wei, kakakin hukumar tsaron jama’a ta birnin Guangzhou ya ce, tilas ne dukkan baki ‘yan kasashen waje dake Guangzhou su mutunta dokokin kasar Sin kuma dole ne su amince da dukkan binciken da za’a gudanar da suka shafi fasfo nasu da sauran muhimman takardu wadanda jami’an tsaron ke tantancewa.
Tun daga ranar 27 ga watan Maris, hukumomin Guangzhou suka umarci dukkan mutanen da suka shiga daga kasashen waje su killace kansu sannan su tabbatar an yi musu gwaje gwajen tantace kwayoyin cutar wato NAT a takaice.
Ya zuwa ranar Asabar, baki daya mutane 4,553 daga kasashen da suka fi barazanar kamuwa da cutar COVID-19 aka yiwa gwaje gwajen NAT a Guangzhou, 679 daga cikinsu suna cibiyoyin lafiya ana kula da su, yayin da mutane 3,771 suna killace kansu a gida.
Ya zuwa tsakiyar daren Asabar, birnin Guangzhou ya samu rahoton mutane 119 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da suka shiga daga ketare, kamar yadda magajin garin birnin Guangzhou Wen Guohui ya bayyana. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)

Exit mobile version