Connect with us

WASANNI

Guardiola Ya San Hanyar Da Zai Bi Ya Doke Madrid, Cewar Silva

Published

on

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a Ingila, Bernado Silva, ya ce farin sanin da kocin Manchester City, Pep Guardiola yayi wa yadda ake buga wasa a kasar Sipaniya zai taimaka wa kungiyar wajen murkushe Real Madrid a haduwa ta biyu da kungiyoyin za su yi a matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai.

Manchester City na sa ran lashe wannan kofi mai daraja a kwallon kafar Turai, amma hakan ba zai samu ba sai ta doke Real Madrid, wacce sau 13 ta lashe wannan kofi a wasa na biyu da zasu fafata a filin wasa na Ettihad dake garin Manchester a kasar Ingila
Real Madrid za ta ziyarci filin wasa na Etihad ne bayan da ta lashe kofin Laligar kasar Sipaniya a karon farko tun shekarar 2017, kuma shi kansa Silba ya san dole sai Manchester City ta yi tsayuwar gwamin jaki idan har tana so ta tsallaka zuwa wasan daf da na kusa da na karshe.
“kwarewar Guardiola ta koyar da manyan kungiyoyi da kuma lashe kofin bugu da kari da buga wasa da manyan kungiyoyin duniya zata taimaka masa wajen doke Real Madrid a wasan da zamu fafata a sati mai zuwa” in ji Silba, dan asalin kasar Portugal
Ya ci gaba da cewa “Real Madrid babbar kungiya ce wadda ta iya buga kofin zakarun turai sannan kuma tana da tarihin lashe kofin sama da kowacce kungiya a duniya saboda haka duk da cewa muna da nasara a kansu a wasan farko ba zamu saki jiki ba”
Guardiola ya horar da kungiyar Barcelona, wacce ita ce abokiyar hamayyar Real Madrid a kasar Sipaniya daga shekarar 2008 zuwa 2012, wadda hakan ya sa Silba ke ganin ya san sirrin da zai kai shi ga murkushe Real Madrid din.
Advertisement

labarai