Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa kociyan Manchester city, pep guardiola yafi kowanne mai koyarwa iya koyarwa.
Chelsea da Manchester city dai zasu fafata wasa a yau a wasan sati na 7 na gasar firimiya bayanda kowacce kungiya tafara gasar da kafar dama a cikinsu duk da cewa Manchester city tana gaban Chelsea da maki uku wadda Chelsea a yanzu itace a matsayi na uku yayinda city take mataki na daya.
Antonio conte ne yalashe gasar firimiya wadda ta gabata duk da cewa Guardiola yana rike da Manchester city, sai dai conte ya bayyana cewa zaman guardiola a kasar ingila yana kara sawa y adage don ganin yana samun nasara.
Conte yace yana ganin girman Guardiola sosai saboda babban koci ne wanda babu kamarsa, kuma yana son ganin kallon wasan kungiyar da giardiola yake koyarwa domin yana karuwa da salon buga wasansa.
Yakara da cewa kowa yasan duk kungiyar da guardiola yake koyarwa tana kokarin ganin tana mallakar kwallo sama da kowa kuma sannan suna kirkirar damar cin kwallo sama da kowa.
Conte yace kowa yasan Manchester city ta kara girma kuma salon buga wasansu ya canja tun lokacin da guardiola yafara aiki a kungiyar.
A kakar wasan data gabata dai Chelsea ce kungiya daya tilo data doke Manchester city gida da waje a gasar firimiya.