An Gudanar Da Taron Yaki Da Tsattsauran Ra’ayi A Abuja

Daga Muhammad A. Abubakar, Abuja

A ranar 15 ga watan Fabrairun 2018 wanda yayi daidai da Alhamis din makon da ya gabata ne Cibiyar Sasanci ta UFUK tare da hadin gwiwar IPCR ‘Institute of Peace and Conflict Resolution’ suka gudanar da taron karawa juna sani karo na 4 dangane da kara dankon soyayya da hakurin zama da juna, wanda aka yi wa take da: “Dakile tsattsauran ra’ayi”.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wurin taron akwai uwargidar Shugaban Kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin Babbar Mataimakiyarta, Hajo Sani.

Aisha Buhari ta bayyana cewa, hakurin zama da juna shi ke kara fahimtar juna da annashuwar rayuwa a tsakanin ‘yan Nijeriya. Sannan ta yi kira ga ‘yan kasa da su kaunaci juna.

Ta ce; “Ina ta kokarin ganin an samu hadin kai a tsakanin ‘yan kasa, duk kuwa da cewa sau da yawa ana kuskure fahimtar jawabai na. Dole ne mu koyi yin hakurin zama da juna.

“Mu kawar da kai daga bambancin addini, bambancin bangaranci, bambancin launin fata, dukkanmu ‘yan Nijeriya ne” inji ta.

Haka nan shi ma, Babban mai masaukin baki, John Cardinal Onaiyekan, ya bayyana cewa da yawan kiristoci sun sauka daga ainihin koyarar kirista, wanda ke koyar da kaunar Allah da kaunar makwabta.

Ya ce: “Ubangijinmu Yesu ya ce mu kaunaci juna, kamar yadda yake kaunarmu, dole ne muma mu kaunaci makabtanmu.”

A nashi jawaban, Babban Daraktan Cibiyar IPCR ‘Institute of Peace and Conflict Resolution’ Farefesa Oshita O. Oshita, ya ce suna yin hadin gwiwa da Cibiyar Sasanci ta UFUK ne saboda kyakkyaar manufar samar da hadin kan da suke da shi.

Shi ma shugaban Cibiyar Sasanci ta UFUK, Kamil Kemanci, ya bayyana cewa makasudin wannan taro shi ne samar da ata kafa acce za a rika musayar ra’ayi domin karfafa kaunar juna da dakile tsattsauran ra’ayi.

 

Exit mobile version