Musa Muhammad" />

Gudumawar Kungiyoyi Wajen Samar Da Zaman Lafiya

A duk lokacin da al’umma suka samu kansu na zama tare, to babu wani abu da ya kamata a sa a gaba kamar hanyoyin da za a bi don a samu zaman lafiya a tsakanin juna.Wannan ya zama wani abu ne da ya wajaba a ce jama’a sun mayar da hankali a kansa, musamman bisa la’akari da irin muhimmancin da zaman lafiya da fahimtar juna ke da shi a tsakanin jama’a, musamman a wuraren da ake cudanye da addinai daban-daban ko kuma kabilu daban-daban.

A irin wannan, akwai matukar bukatar jama’a su tashi tsaye don tabbatar da an samu zaman lafiya da fahimtar juna, inda a wasu lokuta za a ga daidaikun jama’a da kungiyoyi sun dukufa wajen fitowa don yin yekuwa game da muhimmancin wannan abu, ta yadda ake ta yin kiraye-kiraye ga jama’a su rungumi akidar zaman lafiya da fahimtar juna a duk inda suke.

Yana da muhummanci a samu wasu kungiyoyi, wadanda za su rinka shiga tsakanin jama’a suna shirya masu tarukan wayar da kai game da muhimmancin wannan abu, wanda kuma a halin yanzu za mu iya cewa ana samun ci gaba wajen samar da wadannan kungiyoyi.

A irin wannan ne wata kungiya da wasu mutanen kasar Turkiyya, wadanda suke gudanar da ayyukan kasuwanci da taimakon al’umma da yawa a wannan kasa, wato UFUK DIALOGUE ta dukufa wajen gudanar da ayyukan da take ganin za ta wayar wa da jama’ar kasar nan kai wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna.

UFUK DIALOGUE ta kasance tana gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a wurare da dama domin a nuna yadda wannan abu na fahimtar juna ke da muhimancin ga duk al’ummar da zaman tare da ya kama, ba tare da la’akari da addini, kabila ko yankin da mutum ya fito ba.

An kafa kungiyar UFUK DIALOGUE ne a Abuja domin ta shiga gaba don bayar da tata guduamawar wajen samar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Nijeriya, ta hanyar shirya tarurrukan da za a tattauna, a yi musayar ra’ayi a duk hanyoyin da ake jin za su taimaka wajen cimma wannan manufa ta samar da fahimtar juna.

Yana da muhimmanci a san cewa a rayuwa babu wani abu mai muhimmanci kamar samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, domin ta hanyar haka ne ake samun duk wani ci gaba mai amfani ga duk wani mahaluki zai tunai a kansa.

Babu yadda za a a samu wani ci gaba mai ma’ana ba tare da an samu fahmtar juna a tsakanin jama’a ba. Domin da fahmtar juna ne ake samun zaman lafiya, da zaman lafiya ne ake samun duk wani ci gaba mai amfani ga al’umma da duk wani mai rai.

A yawancin lokuta rashi kusantar juna ne babban jigon kawo duk wani sabani da rashin jituwa. A irin wannan ne ya sa ita wannan kungiya ta UFUK DIALOGUE ta fi mayar da hankalinta wajen shirya abubuwan da za su kusanto da jama’a kusa domin a ji daga juna, a fahimci juna, a magance duk wani sabani da ka-iya kawo rudani a tsakanin jama’a.

Na kasance cikin wadanda wannan kungiya ta UFUK DIALOGUE ta gayyata wajen wani babban taro da ta kira a watannin baya, bisa hadin kwiwa da wasu Hukumomi domin shirya wani babban taro na kasa da kasa don tattauna muhimman batutuwan da suka shafi wannan maudu’i namu na samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, inda a bana aka hada da karama wasu fitattu wajen taimaka wa samar da zaman lafiya.

Ga duk wanda ya halarci wannan taro, lallai ya tafi da tunanin cewa babu wani abu a rayuwa da ya fi al’umma su fahimci muhimmancin zaman lafiya, ta hanyar fahimtar juna, zaman tare da duk masu ra’ayi kowne iri ne, da kuma duk masu kowace irin fahimta ce. Domin an tattauna batutuwan da suka shafi wannan harka, ta yadda za a iya shiga gaba a jagorancin duk wani nau’i na wannan abu.

Saboda haka lallai akwai matukar bukatuwa ga jama’a su kafa irin wadannan kungiyoyi don shiga cikin al’umma ana shirya masu taruka don wayar da kai game da muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna, wanda da haka ne akwai ake samun duk wani ci gaba mai amfani da ake nema.

Kamar yadda na taba fada a Wani rubutu da na yi a makwannin baya, inda Na yi bayanin cewa su ma al’umma suna da Matukar bukatuwa su samar da irin wadannan Kungiyoyi da za su taimaka wajen Wannan aiki.

Wasu gwamnatoci sun riga sun samar da irin wadannan Kungiyoyi/Hukumomi, wadanda aka dora wa alhakin gudanar da yekuwa don samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, wanda shi da ma ya yi fice wajen Wannan aiki, ya kafa Hukumar ‘Peace Commission,’ wadanda kuma suka dukufa wajen Wannan aiki na samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

In Allah ya yarda zan sami lokaci in yi rubutu Na musamman game da wannan Hukuma ta ‘Peace Commission.’

 

Exit mobile version