Musa Muhammad" />

Gudumawar ’Yan Sintirin Sa-kai A Harkar Samar Da Tsaro

Kamar yadda na sha fada a rubuce-rubucena, daya daga cikin manyan abubuwan da suka hau kan Hukuma, wadanda suke kuma muhimmai, shi ne harkar samar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a, musamman  a wannan lokaci da lamura suka lalace a kasar nan.

Kamar yadda yake, wasu Gwamnoni da sauran shugabanni sun dukufa wajen ganin sun sauke wannan nauyi da ke kansu, inda suke fito da hanyoyi daban-daban wadanda suke ganin za su taimaka wa jama’a wajen samar da tsaro a wutaren da suke.

Haka su ma al’umma, ganin cewa ‘in dambu ya yi yawa ba, ya jin mai,’ abubuwan nan suna yi wa gwamnati yawa, don haka sai su ma sukan fito da wasu hanyoyin da suke ganin za su taimaka masu wajen samar da dan abin da za su iya na tsaron rayukansu da dukiyoyi.

Ta irin wannan ne ake kafa wasu kungiyoyin tsaro na sa-kai, wadanda za su rinka kula, tare da sa ido a harkar tsaron yankunan nasu. Inda kuma akan ba wadannan kungiyoyi sunaye daban-daban, ya danganta da Unguwa.

Wasu lokuta, duk da amfanin irin wadannan kungiyoyi, amma idan ya zama ita Hukuma ta lura da cewa wasu na neman yin amfani da wadannan kungiyoyi wajen cin zarafin al’umma, ko kawo wata rashin jituwa a tsakamin jama’a, ta kan taka wa abin abirki, ta hanayar soke su ko kuma shiga ciki don ta kawo gyara.

A irin wannan ne nake ganin ya sa gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jargorancin Malam Nasiru Ahmad El-rufai ta guji irin wadannan abubuwa, ta kafa tata Hukumar sintirin, wadanda za su zama a Unguwanni domin taimaka wa jami’a tsaro wajen sa ido a duk wani abin da ya shafi harkar tsaro a jihar, inda kuma ba tare da bata lokaci ba ta soke duk wata kungiyar sintiri.

Kamar yawancin matakan da gwamnati kan dauka, shi ma wannan matakin ya samu suka daga wajen wasu al’umma, inda kuma wasu ke ganin gwamnati ta yi abin da ya dace, musamman yadda ake tunkarar babban zaben 2019, wanda suke ganin idan ba a yi wa tukka hanci da wuri ba, to abubuwa ka iya zama wani abu.

Jama’a da dama na ganin cewa wannan mataki da gwamnatin ta dauka ya yi daidai, domin zai taiamaka wajen saita duk wansu masu ganin za su yi amfani da irin wadanan kungiyoyi don cimma muradun kansu. Tare kuma da ganin cewa ita gwamnatin ba ta bar jama’a haka nan ba, sai ta kafa tata kungiyar, wacce kuma ta nemi wadancan kungiyoyi su shigo cikin wannan sabuwar a tafi da su.

A ’yan watannin baya, Mataimakin Gwamnan jihar Kaduna, Mista Barbabar Bala Bantes ne ya yi jawabi a wurin wani bikin kaddamar da wannan sabuwar Hukuma ta ‘yan sintirin, mallakin gwamnatin jihar Kaduna, wanda ya yi jawabi a madadin Gwamnan, inda ya bayyana cewa an yi wannan abu ne don a samu damar sauke nauyin da ke kansu na samar da tsaro ga al’umma. Sannan ya bayyana soke duk wata kungiyar sa-kai a harkar tsaro a jihar in ba wannan ba.

Wannan sabuwar kungiyar tsaro da gwamnatin ta kafa, wacce za a rinka kira da ‘Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna’ (Kaduna State Bigilance Serbice), an kaddamar da ita ne a ranar wata Litini da ta gabata a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa, “wannan Hukuma an kirkireta ne don a inganta tsaro a jihar, al’ummarmu su zauna cikin aminci a kokarin da suke yi na neman na kansu don kula da kansu da iyalansu. An yi Hukumar ne don ta taimaka wurin inganta tsaro a garuruwanmu da Unguwanninmu.”

Ya ci gaba da tabbatar da cewa, “wannan yunkuri na kafa wannan Hukuma, wani mataki ne na zuba jari wurin tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarmu. Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna za ta taimaka wa sauran Hukumomi na jami’an tsaro.”

Haka kuma Gwamnan ya ce, sun lura da abubuwa da dama wajen kafa wannan Hukumar, ya ce “bisa la’akari da irin fadin kasa da yawan al’ummar da muke da su a jihar nan, muna iya cewa matsalar tsaro ita ce ta fi damunmu, wanda ke sa asarar rayuka da dukiyoyi saboda karancin jami’an tsaro na ‘yan sanda da ake da su.”

Ya ce, “matsalar karancin ‘yan sanda matsala ce ta kasar baki daya, wanda miyagun mutane ke amfani da damar don cutar da al’umma. Saboda haka, maimakon mu rungume hannuwanmu muna jiran gwamnatin tarayya ta samu kudi ta dauki sababbin ‘yan sanda, ko kuma jiran dokar da za ta ba jihohi damar yin nasu ‘yan sandan, sai muka yi wannan tunanin.”

Ganin cewa harkar tsaron na da muhimmanci, Gwamnan ya ce, “bisa wannan dalili ya sa a shekarar 2016, gwamnatin Jihar Kaduna ta yi dokar da ta ba ta damar kafa Hukumar sintiri don taimaka wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro don magance matsalar ayyukan ta’addanci a garuruwanmu da Unguwanninmu. Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna za ta yi aiki Kafada da kafada da Jami’an Tsaro na ‘yan Sanda da sojoji da sauran jami’an tsaron gwamnatin tarayya, musamman a wurin samar da bayanai na sirri.”

Don haka sai Gwamnan ya tabbatar wa da al’ummar jihar Kaduna cewa, “wannan gwamnatin ba za ta bari wasu haramtattun kungiyoyi su yi amfani da wannan  dama da sunan tsaro su tayar da fitina ba. Zan so in yi amfani da wannan dama wurin sanar da jama’a cewa wannan Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna doka ce ta kafata, kuma ita daya ce kawai gwamnati ta san da ita. Saboda haka muna rokon al’umma su ba su hadin kai.”

Daga nan Gwamnan ya sanar da soke duk wata kungiyar tsaro ta sa-kai a duk fadin jihar. Ya ce, “doka ba ta san da wata kungiya ta sintiri ba, in banda wannan. Don haka kungiyoyin sintiri kamar su: Kato da Gora, Cibilian JTF, CESSCUR, Neighborhood Watch, Bigilante Group of Nigeria, Edtreme Security, Jarumai da Gora, ‘Yan Committee, Ujumeme, ‘Yan Tuba da sauransu, duk haramtattu ne.”

Ba a nan Gwamnan ya tsarya ba, sai da ya ba jami’an tsaro umurni, ya ce “sannan ana kiran jami’an tsaro su cafke duk wani da zai fito yana amfani da sunan irin wadancan haramtattun kungiyoyi. Su kuma kungiyoyin da mambobinsu, ana kiran su da su zo su hada kai da Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna don ganin an magance tsaro a Jihar.”

Shi ma Kwamandan wannan Hukuma, wani tsohon dan Majalisar Dokokin jihar Kaduna, masani a harkar tsaro, Hon. Muhammad Ali ya tofa albarkacin bakinsa a wurin taron, inda ya fara da nuna godiya ga Allah da ya nuna  masu wannan rana, wacce ya ce rana ce mai muhimmanci a garesu ’yan wannan Hukuma ta sintiri, domin rana ce da aka ba su cikakken ikon gudanar da ayyukansu.

Muhammad Ali ya ce, “ina matukar farin ciki da wannan tuta da Mai girma Gwamna ya ba ni a wannan rana, wanda ya nuna irin ikon da aka ba mu, wanda kuma zai taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu ba tare da nuna sani ko sabo ba.”

Don haka ne nake ganin idan muka yi la’akari da wadannan bayanai da Gwamnan ya yi a wannan wuri, za mu fahimci yadda ya sa harkar tsaro a gaba, tare da neman hanyoyin da za su kawo tsaron da kuma ingantuwarsa a duk fadin jihar. Muna fatan kwalliya  za ta biya kudin sabulu, musamman ganin yadda zabe ke karatowa, wanda a nan ne ake ganin za a fi bukatar wadannan jami’ai.

Amma sai dai duk da wannan mataki na gwamnatin, wasu jama’a na da ra’ayin cewa bai kamata a soke wadannan kungiyoyi gaba daya ba, domin su ma suna bayar da tasu gudumawar wajen tallafa wa gwamnatin a harkar tsaron. Don haka ne ake ganin ya kamata a sake duba lamarin don a yi gyara, ta yadda za a yi wani tsari da za a tafi da su.

Exit mobile version