Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya

byCMG Hausa
3 years ago
Duniya

A wannan lokaci da muke cikin yanayi na dunkulewar al’ummun duniya wuri guda, hidimomin sadarwa na da matukar muhimmanci, kasancewar suna bude karin kofofin raya tattalin arziki, da kyautata zamantakewar al’ummu daban daban. Kaza lika damar sadarwa tsakanin al’ummun duniya ta riga ta zama daya daga cikin hidimomi masu daraja na more rayuwar bil adama.

Hakan ne ma ya sa karkashin kyawawan manufofin kasar Sin, gwamnati ke karfafa gwiwar sassa daban daban, musamman kamfanonin kasar da su tallafa, wajen bunkasa samar da ababen more rayuwa ga al’ummun duniya a duk inda suke.

  • Yadda Kasashe Masu Ci Gaba Za Su Cika Alkawuransu Yana Da Muhimmanci Wajen Kare Muhallin Duniyarmu

A baya bayan nan, kamfanin ayyukan fasahar sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya alkawarta hade sassan al’ummun duniya miliyan 120, dake rayuwa a wurare masu wuyar kai wa, a kasashen duniya da yankuna sama da 80 da layukan sadarwar wayar tafi-da-gidanka, nan zuwa karshen shekarar 2025.

Fatan kamfanin shi ne kara fadada gajiyar sadarwar wayar hannu ga al’ummun duniya, ta yadda za su ci riba daga fasahohin bunkasa tattalin arziki, da kasuwanci, da inganta sha’anin zamantakewa, da dasa tunani mai kyau a fuskar samar da ci gaba mai dorewa.

Dama dai ya zuwa karshen shekarar 2021, kamfanin na Huawei, karkashin shirinsa na “RuralStar telecom solutions”, wato shirin samar da turakun sadarwar salula a kauyuka, ya rika ya hada sama da mutum miliyan 60 dake rayuwa a wurare masu wuyar shiga, a kasashe da yankunan duniya sama da 70 da layukan wayar hannu.

Ba shakka irin wannan tunani, na fadada damar al’ummun yankunan karkara, da mutanen dake zaune a wurare masu nisa, na samun hidimomin wayar sadarwa da kamfanin Huawei ke aiwatarwa abun a yaba ne. Kuma wata muhimmiyar hanya ce da kamfanonin Sin ke bi wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin al’ummun duniya, musamman al’ummun kasashe masu tasowa. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Ba Zan Koma APC Ba – Mataimakin Tambuwal

Ba Zan Koma APC Ba - Mataimakin Tambuwal

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version