Abdulrazak Yahuza Jere" />

Gudummawar Shugabannin Addini Ga Yaki Da Cutar Korona

Annobar Cutar Korona, na cigaba da yaduwa a sauran sassan duniya. Tun bayan bullar wannan mummunar cuta dai a Wuhan da ke Kasar China, sama da mutane dubu 170,000 ne suka rasa rayukansu, a cikin mutane Milyan 2.4 da suka kamu da wannan cuta a akalla kasashe kusan 185, inda kuma kimanin mutane 651,000 suka warke.
Domin kokarin dakile yaduwar wannan cuta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sanya dokar hana fita a Jihohin Legas, Ogun da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, inda daga bisani kuma wasu jihohin su ma suka biyo baya.
Har ila yau, duk da wannan namijin kokari da Gwamnatin Tarayya ke yi akan dakile yaduwar wannan cuta, amma sai kara yaduwa take yi a fadin wannan kasa. Kazalika, Sakataren Gwamnatin Tarayya wanda kuma shi ne Shugaban tawagar yaki da wannan mummunar cuta na kasa ya bayyana cewa, shirye-shirye a Nijeriya sun yi nisa domin kawo karshen wannan annoba.
Haka nan, wannan gidan Jarida ya lura tare da bayyana rashin jin dadinsa, duk da kasancewar wanzuwar wannan annoba da kuma adadin mutanen da ta kashe wadanda ke dauke da wannan cuta, amma wasu Malamai ko jagororin addini na cigaba da yin watsi da dokokin da gwamnati ta gindaya, musamman a wuraren yin bauta (Masallatai da Coci-coci).
Misali kamar a Abuja, akwai Malamai ko Limaman da aka cafke sakamakon karya ire-iren wadannan dokoki da gwamnati ta gindaya na hana taruwar mutane wuri guda. Tawagar da ta kai wannan simame karkashin jagorancin Kwamared Ikharo Attah, sun dira kai tsaye Masallacin Juma’a na Wuye tare da cafke babban Limamin Masallacin. Kazalika, Attah ya sake bayyana cewa, sun samu rahotanni da dama na wasu Limamai da suka gudanar da Sallar Juma’a a wannan lokaci na hana zirga-zirga a Abuja. Haka nan, wannan tawaga ta Jami’an tsaro ta sake samun nasarar cafke wasu Fastoci a dai Abujan wadanda suka yi watsi da wannan doka ta gwamnati na hana zirga-zirga tare da hana hada kowane irin taron mutane.
Sa’annan, mun samu labarin cewa akwai wasu Gwamnoni wadanda suka yi amfani da addini wajen baiwa Kiristoci damar aiwatar da bautarsu, musamman a ranar bikinsu na Ista tare da kyale Musulmi su cigaba da aiwatar da sallarsu ta Juma’a kamar yadda suka saba yi.
Saboda haka, ya kamata a lura cewa hatta Kasar Saudiyya wacce ita tushen Addini Musulunci, ta dakatar da yin salloli a Masallatanta na Hamsul salwati da kuma Sallar Juma’a a ciki da wajen dukkanin Masallacin Makka da Madina, domin dakile ko hana yaduwar wannan cuta ta Korona. Sannan, an dakatar da ibadar da aka saba yi duk shekara, wato Umra a Makka.
Har wa yau, duk girman Masallacin Makka, wanda Musulmi ke tutiya da shi, yau an rufe shi. Sannan, an baiwa kowa da kowa umarnin ya koma gida ya yi sallarsa a wannan wata na Azimi, haka nan ko da bikin Sallah Karama ma, kowa a gidansa zai yi indai har wannan cuta ta Korona za ta cigaba da yaduwa a tsakanin al’umma.
Haka nan, shi ma Fafaroma a lokacin bikin Ista, bai yarda an hada dandazon mutane a wuri guda ba, sakamakon wannan mummunar annoba ta Korona wadda ta addabi duniya baki-daya. Kiristoci na girmama wannan rana ta Ista tare da ba ta muhimmancin gaske, amma haka Fafaroma ya hakura da wannan taron biki da suka saba yi duk shekara.
Abin haushi da takaici shi ne, yadda muka fahimci cewa wasu daga cikin Shugabannin addini da Gwamnoni har yanzu ba su fahimci mummunar illar wannan cuta ba. Domin kuwa, da dama daga cikinsu kamar ma ba su yarda da cutar ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda suke tara mabiyansu suke suna karyata wannan cuta ko annoba.
Babban misali a nan shi ne, idan aka lura da yadda wadannan Shugabannin Addini suke juyarwa da mabiyansu kwakwalwa ko tunani, musamman idan aka lura da abinda ya faru da wasu Matasa a Karamar Hukumar Kusada da ke Jihar Katsina, inda suka yi ta faman fafatawa da ‘Yan Sanda a lokacin da suka yi yunkurin cafke wani Limami, wanda ya yi watsi da dokar da gwamnati ta gindaya na hana kowane irin taron addini da sauran makamantansu.
Saboda haka, magana ta gaskiya idan har Kasashen Musulunci kamar Saudiyya za su dakatar da kowane irin taron addini, me zai hana Musulmi da Kiristocin Nijeriya su bi dukkanin dokokin da kasa ta gindaya, domin dakile hana yaduwar wannan mummunar cuta?

Exit mobile version