Abubakar Abba" />

Gudummowar Da Kafafen Yada Labarai Za Su Bayar Wajen Yaki Da Ta’addanci A Nijeriya

Ba za a taba samun nasarar yaki da ta’addanci ba, sai da taimakon kafafen yada labarai. A kan haka ne TARKAA DABID ya shirya rahoto na musamman wanda ya bayyana gudummowar kafafen yada labaran wajen samun nasarar tsaron kasa da yaki da ta’addanci, musamman da yake daga kafafen yada labaran ne al’umma ke samun bayanan abubuwan da ke faruwa na yau da kullum tare da ilimantar da su kan haradin da ke tattare da ta’addanci. Sabo Ahmad  Kafin-Maiyaki ne ya fassara rahoton Daga Jaridar LEADERSHIP ta Ingilisi ta ranar Juma’ar da ta gabata,  domin amfanin masu karatunmu.

Ko shakka babu, alamarin tsaro abu ne da ke da sarkakakiya tare manayan kalubale , saboda haka ma kafafen yada labarai ked a matukar muhimmanci wajen yaki da ta’addanci a dukkan fadin duniyar nan.

Saboda haka, yana da matukar muhimmanci mu fahimci irin gudummowar da kakfafen yada labarai za su iya bayarwa wajen yaki da ta’addanci, musamma da yake suna iya isar da sako mai kyau ko mara kyau. Ya zama wajibi mu fahimci haka domin ta hanyar kafen yada labarai ne ake isar da sako a ko’ina a fadin duniyar nan.

Yanzu haka an fahimci cewa, bayan yakin da sojoji ke yi da ta’addanci, akwai bukatar jawo kafafen yada labarai wajen ilimantar da jama’a kan illar da ke tattare da ta’addanci wanda hakan zai taimaka wajen samun nasarar yaki da ‘yanta’addan da ke fadin kasar nan.

Haka kuma, dole ne a kai sojoji musamman jihohin Arewacin kasar nan wadanda za su nemi gudummowar samun bayanai daga jama’a da za su taimaka wajen samun zaman lafiya.

Tun lokacin da rundanar sojojin Nijeriya ta daura damarar yaki da ‘yan ta’adda aka samu hadin kai tsakanin sojojin da kafafen yada labarai, wanda hakan ke taimakawa wajen samun nasara kan manufar da ake da ita.

Haka kuma sabbin dabarun yakin da sojojin ke bullowa da su, na dada jefa ‘yan ta’addan cikin halin tsaka-mai-wuya, saboda haka domin kawo karshen wannan ta’adanci, sai an kara daura ramara sosai.

Saboda haka, ganin yadda jama’a suka rungumi kafafen yada labarai wajen samun bayanai, ya nuna irin gudummowar da za su iya bayarwa wajen yaki da ta’addanci.

Shugaban rundunar taron sojojin Janar Gabriel Olanisakin ya bayyana a wajen wani taron karawa juna sani da aka shiryawa ‘yan jarida masu daukar labaran tsaro a Abuja, cewa, akwai babban kalubale da ke gabansu saboda haka su tabbatar da cewa, sun iya fuskantar wannan kalubale.   

Ya ce, yana aikin soja na bukatar hadin kai da kafafen yada labarai, domin su  ci gaba da fadakar da jama’a kan tsaron kasa, domin al’umma na dogaro da kafafen yada labarai  wajen sanin halin da kasa ke ciki, saboda haka za su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin zama lafiya.

Haka kuma ya ci gaba da cewa, a wannan lokacin da ake da hanyoyin isar da sakwanni ta kafafen yada labarai na zamani, akwai bukatar wadannan kakafafen yada labarai su ci gaba da bayar da gudummowarsu wajen ci gaba da wayar da kan jama’a.

Exit mobile version