Muhammad Maitela" />

Gudummowar Sojoji Wajen Samar Da Tsaro

Al’ummar Nijeriya sun dade suna cikin zullumi, sakamakon karuwar aikata miyagun laifuka a fadin kasar. Domin ganin an kawo karshen aikata wadannan miyagun laifuka, jami’an tsaro sun tashi tsaye  ba dare ba rana don kakkabe bata-tagari ta tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a kasa, TARKAA DABID ya dubi yadda kokarin da rundunar sojojin Nijeriya  ke wajen tabbatar da tsaron kasa da kuma kare iyakokin Nijeriya daga shigowar bata-gari, Muhammad Maitela, Damaturu ne ya fassara domin amfanin masu karatunmu. A sha karatu lafiya:

Yayin da samar da tsaron cikin gida tare da diyaucin ta daga kowanne irin katsalandan da kutsen wasu daga ketare zai ci gaba da bunkasa a hannun sojojin Nijeriya, lamarin da wani lokaci yake da bukatar hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron cikin gida.

Wanda ba wani tantama, kan cewa, a halin da ake ciki yanzu, Nijeriya tana fuskantar matsalolin tsaro, kama daga wadda ta taso ta dalilin matsalar tsaron Boko Haram, da wasu kungiyoyin tayar da kayar baya, irin su yan bindiga da masu garkuwa da jama’a tare da makamantan su. Haka kuma, sojojin Nijeriya su ne wadanda nauyin samar da tsaron kasa, domin su ne aka dora wa alhakin kare kasa daga kowane irin kutse daga waje, tare da bayar da gagarumar gudumawa a lokacin yaki da Boko Haram, kungiyar da barazanar ta bata takaita ga tu’annati ga tattalin arzikin kasa ba kawai, hatsarin ta ya hada da kokarin raba kan yan kasa.

Rundunar sojoji, a kowane lokaci aikin da suka fi bayar da muhimmanci a kan sa shi ne yaki da aikace-aikacen mayakan Boko Haram tare da masu tada kayar baya da dangogin su, yayin da wannan aikin samar da tsaro ya jawo wa Nijeriya asarar biliyoyin naira tare da rasa dimbin rayukan yan kasa.

Wanda hakan ya tilasta wa sojojin Nijeriya damn takon saka da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama, irin su ‘Amnesty International’, kungiyar da ta sha kalubalantar aikace-aikacen da sojojin ke yi na yaki da yan kungiyar. Lamarin da ya jawo wasu dora zargin cewa mayakan suna samun tallafin wasu kasashen ketare don su yaki Nijeriya, kamar yadda ministan tsaro, Mansur Dan-Ali.

Ya ce, akwai zargin cewa wadannan mayakan suna samun horon musamman da tallafin kudi daga takwarorin su ciki da wajen Afrika tare da kira ga gwamnatin kasar Rasha da ta kawo wa rundunar sojojin dauki domin ganin bayan wannan matsala ta tsaro a yankin.

Ministan tsaron, ya yi wannan furucin a birnin Moscow, tare da bayyana cewa, “tun a 2009, kasar mu ta Nijeriya ta fada gararin matsalar tsaron rikicin Boko Haram. Wanda mayakan ke kaddamar da mabambantan hare-haren bama-baman a wurare daban daban tare da halaka dimbin jama’ar da basu ji ba basu gani ba.

“dadin dadawa kuma, ta yaki da wannan matsala ta tsaro a Nijeriya ke gudanar wa a karkashin hukumar kula da tabkin Chadi, wadanda suka kunshi Benin, Niger, Chadi da Kamaru, domin kyautata sha’anin shugabanci da kyautatuwar lamurra a yankin”.

Har wala yau kuma, ministan ya yi kira ga kasa da kasa da su hada karfi da karfe wajen tunkarar wannan matsala ta tsaro, domin samun nasarar gamayyar jami’an tsaron kasashen duniya a wannan yanki na zirin tabkin Chadi. Ya ce Nijeriya ta na lissafa kasar Rasha a matsayin babbar kawa a wannan yaki da Boko Haram.

“muna matukar farin-cikin kasancewar kasar Rasha a matsayin kwararriya a wannan fagen, wajen ganin bayan wannan matsala ta yan aa’adda. Saboda wannan, zamu yi matukar farin -cikin samun tallafin soja da na kwararru ta wannan haujin, matuka”. Inji shi.

Dan-Ali ya sake nanata cewa, Nijeriya ta na matukar jin dadin goyon bayan da gwamnatin Rasha ke bata shekara da shekaru, ta fuskar horo, tallafin karatu tare da habaka harkar tsaro ta hanyar na’urarorin zamani na kimiyya da fasaha.

“haka kuma, Nijeriya tana kokari wajen kirkiro hanyoyi tare da matakan farfado da alakar huldar kasuwanci da zuba jari a kasar mu, domin fadada kasuwanci wanda hakan zai jawo kwalliya ta biya kudin sabulu- a wannan hulda tamu”.

“wanda ta wannan dalili ne ya jawo Nijeriya ke matukar burin samun taimakon kasar Rasha ta bangaren kimiyya da fasaha ga sojojin mu tare da sauran sassa”.

Haka kuma ya shaidar da cewa, Nijeriya tana da bukatar tallafi wajen sake farfado da muhimman ayyukan ci gaban kasa, tare da kyautata ayyukan soji a zamanance. Kuma Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa da martabar ta wadda ta cancanci girmamawa, saboda haka, duk wani tashin-tashina da wasu ke kokarin ingizawa,  bai wuce wasan yara ba. Kuma akwai wadanda ke cin gajiyar rura wutar wannan rigima don kasar ta shiga garari, musamman irin Zamfara, Filato da yankin hako man fetur a Nija Dalta.

“A zaton da muke yi, rundunar sojojin Nijeriya ta koka dangane da yadda wasu kasashe ke kokarin amfani da matsalar tsaro domin biyan burin kashin kan su, ta hanyar daukar nauyin yan ta’adda da dangogin su. Wanda sojojin suka gano wasu bata-gari ke kokarin kawo cikas a bukin rantsar da zababbun shugabanin zaben 2019”. In ji shi.

A wani batu na daban kuma, mukaddashin jami’in hulda da jama’a a rundunar sojan Nijeriya, Kanal Sagir Musa, ya bayyana cewa, rundunar sojin ta bankado take-taken gungun wasu bata-gari wadanda ke samun taimakon wasu kasashen ketare da nufin tayar da hankula ta hanyar hargutsa Nijeriya da wani yanki na Afrika.

Ya kara da cewa, wadannan maras kishin kasa, suka kokarin yin amfani da bangarorin yan ta’adda na ISWAP/Boko Haram da yan barayin shanu da dangogin su ta hanyar kudi domin tayar da hargitsi.

“mun samu bayanai daga majiya mai tushe wadda ta tabbatar mana dangane da yadda wasu ke kokarin yin amfani da mayakan Boko Haram, kuma da gangan tare da wasu kuma masu kokarin yada labaran karya tattare da sojojin da hada husuma tsakanin jami’an tsaro da jama’a tare da gwamnati”. Ya bayyana.

“haka zalika kuma, daukar wannan matakin bayanin kwarmata lamarin ya zama dole tare da jan hankali ga wadannan mutanen ko gungun kungiyoyin, wanda yin biris da wannan gargadin zai kai ga su yaba wa aya zaki”. Ya nanata. Ya kara da cewa, akwai hannun wasu kasashen wajen wajen haifar da rikicin ta amfani da wadannan kungiyoyin.

“dadin dadawa kuma, muna wannan bayanin a matsayin mu na sojojin Nijeriya, wadanda a kowane lokaci nauyin kare tsaron kasa da yan kasa tare da shiga tsakani domin warware duk abinda zai kai ga samun sabani. Kuma muna zuba idanun mu fiye da kowane lokaci, wajen gudanar doka da oda tare da kare diyaucin Nijeriya daga kutsen ciki da wajen kasa”.

Har wala yau kuma, ya shawarci yan Nijeriya kan su mutunta diyaucin kasar su tare da dokokin da suka kafa kasar, “wanda a matsayin mu na kasa mai zaman kanta, yana da gayer muhimmanci sojoji su dauki matakan difolomasiyya da amfani da kwarewa wajen dakile kutaen wasu kungiyoyin kasashen ketare tare da farfado da zaman lafiya.  Wanda bai kamata mu ci gaba da rayuwa a cikin zullumi ba, saboda bamu san abinda zai kai ya komo ba”.

Exit mobile version